MU SAN ANNABINMU (26)

Salati da amincin Allah su tabbata bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan mabiyansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Acikin wannan darasin na Zauren Fiqhu zamu dora daga inda muka tsaya acikin tarihin Manzon Rahama (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

YAQIN HAMRA'UL ASAD :

Washegarin dawowa daga yaqin uhudu sai Manzon Allah (saww) yayi tunanin watakil mushrikan Quraishawa su sake kawo hari garin madeenah don haka yayi nufin fita domin sake tararsu a sake wani sabon gumurzu don a nuna musu cewa har yanzu fa musulunci yana nan da Qarfinsa.

Ashe kuwa shi Abu Sufyan shugaban dakarun Quraishawa ya daura niyyar dawowa din don Qara kawowa hari akan Musulmai, akan hanyarsa sai ya hadu da wani mutum mai suna Ma'abadu 'dan Ubayyu Alkhuza'iy. Sai Abu Sufyan din ya tambayeshi "Meye labarin abinda ke bayanka?".

Sai yace masa "Ya kai Abu Sufyan, yi sauri ka guje daga garesu domin hakika sun tanadi makamai domin yaqarku".

Daga jin haka sai tsoro ya cika zukatan mushrikan suka juya zuwa garinsu.

Garin Hamra'ul Asad yana da nisan Mil takwas daga garin Madinah. Kuma Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya isa wajen tare da rundunar Sahabbansa, sun zauna tsawon kwanaki uku awajen, sannan suka juya zuwa garin madinah bayan sun tabbatar da cewa Mushrikan sun janye daga mugun nufinsu.

YAQIN BANUN NADHEER :

Wannan yaqin ya afku ne acikin shekara ta hudu bayan hijirar Annabi (alaihis salam). Kuma Banun Nadheer sunan wata babbar kabilah ce daga kabilun yahudawan yankin larabawa. Kuma suna zaune ne daga chan saman garin Madinah.

Kuma abinda ya janyo wannan yaqin shine watarana Manzon Allah (saww) ya fita zuwa garin Yahudawan tare da wasu Sahabbansa, yaje domin neman agaji awajen Shugbanninsu su taimaka masa wajen biyan diyyar wasu mutane biyu wadanda Musulmai suka kashesu bisa kuskure.

Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya zauna akarkashin wata katanga yana hutawa kenan sai Yahudawan suka ha'da baki akan cewa wani daga cikinsu zai hau ta bayan katangar sannan ya jefo wani marga-margan dutse akan Manzon Allah (saww) suyi masa kisan gillah. (kunji makircin yahudawa fa).

Shi kuwa Manzon Allah (saww) tuni Ubangijinsa ya sanar dashi game da abinda yahudawan ke shiryawa. Don haka ya tashi ya koma garin Madinah sannan ya turo musu 'dan aikensa mai suna Muhammad bn Maslamah Al Ansariy (Allah ya yarda dashi). Da sakon cewa "Hakika Manzon Allah (saww) ya aikoni gareku cewa :

"KU FICE MUN DAGA GARINA DOMIN HAKIKA KUN KARYA ALKAWARIN DA NA SANYA MUKU TA DALILIN YAUDARAR DA KUKA YI NIYYAR YI GARENI. NA BAKU KWANA GOMA (KU FICE) BAYAN NAN DUK WANDA AKA GANI DAGA CIKINKU ZA'A SARE WUYANSA".

Saboda taurin kai irin nasu sai suka Qi ficewa har kwanaki goman nan suka wuce. Don haka sai Manzon Allah (saww) ya fita tare da Sahabbansa suka kewaye garin Yahudawan (ba shiga ba fita).

Da suka ji wahala dolensu suka mika wiya bisa alkawarin cewa zasu fice tare da iyalansu da dukiyoyinsu amma ba zasu dauki makamai ba. Annabi (saww) ya basu dama suka fice. Wannan shine karshen zaman yahudawan banun nadheer a yankin garin Madinah.

Anan zamu dakata sai a darasi na gaba kuma. Da fatan Allah shi Qara mana lafiya da zaman lafiya da kwanciyar hankali a garuruwa da unguwannin musulmai baki daya. Allah yasa mu shiga watan Ramadhan a sa'ah.

An gabatar da karatun a ZAUREN FIQHU WHATSAPP ranar 19/08/1440 25/04/2019.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI