MAGANIN TSAGEWAR FATAR TAFIN HANNU DA SAURAN CIWUKAN DAJI :
TAMBAYA TA 2621
*******************
Assalamu Alaikum, Malam barka da rana ya iyali? Allah saka maku da aljanar firdaus akan taimakon dakukeyi amin. Malam yarona ne yake fama da kuraje a tafukan hannun shi kurajan suna fitowane kamar bororon Wuta, wani lokaci kuma sai sufito kanana ko kuma haka kawai sai hannuwan su rinka tsagewa kamar ya yanke kuma suna Mashi kaikai Dan wani lokaci kaikain yakan hanashi bacci sosai idan kuma ya Sosa sai su rinka fitar da jini.Malam dan Allah ataimaka mana, daga dalibarku.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah.
Irin wadannan chutukan fata ne kuma basu rasa alaqah da ciwon daji irin na fata. Amma ga wasu abubuwa nan ki jarrabah.
1. Ki samu lalle (irin wanda kuke yin Qunshi dashi) ki kwaba da ruwa amma ki sanya man zaitun kamar cokali guda aciki. Sai kiyi masa Qunshi a hannayen nasa.
Lalle yana maganin mafiya yawan ciwukan fata. Kici gaba da yi masa Qunshin duk bayan sati biyu. In shaAllah cikin Qankanin lokaci Qirajen zasu dena fitowa kuma hannun zai dena tsagewa.
2. Ki samu kwakwa kiyi blending dinta, ki tache ruwanta kamar cokali uku ki zuba acikin ruwan zafi rabin kofi. Idan yayi sanyi sai ku bashi yasha da safe kayin ya karyawa (breakfast) da minti 20.
In shaAllah wannan ruwan kwakwan zai kashe kwayoyin chutar Qurajen dake cikin cikinsa. Kuma idan zai kwanta barci ki shafa masa man kwakwar a kan tafin hannayen nasa da sauran wuraren da kurajen suke fitowa.
Masu fama da kurajen fuska ko tautau ko makero ko Qazzuwa, ko ciwon daji ajikinsu duk zasu iya jarraba wannan fa'idar. Kuma in shaAllah za'a samu waraka.
Wallahu A'alam.
DAGA ZAUREN FIQHU (14/04/2019 08/08/1440).
Comments
Post a Comment