LABARIN DAMO YANKAKKE

DAGA ZAUREN FIQHU :

Wani Balaraben Qauye ya farauto Damo (alligator) ya shigo gari sai yaga Manzon Allah (saww) tare da wasu Jama'a yana yi musu wa'azi.

Da yaga haka sai ya tambayi mutane "Wannan mutumin fa? wanene?".

Sai akace masa "AI ANNABI NE".

Saboda haka sai Balaraben Qauyen nan ya rika keta tsakanin jama'a, har sai da yazo ya tsaya agaban Manzon Allah (saww). Sannan yace:
"Na rantse da lata da uzza (sunayen gumakansa ne) babu mutumin da na tsaneshi fiye da kai, Ba don kar mutanena su washeni ba, da sai na kasheka".

Sayyiduna Umar bn Khattab (ra) zai zare takobi ya kasheshi sai Manzon Allah (saww) ya hanashi.

Balaraben Qauyen nan ya fito da damonsa (yankakke) daga cikin jakarsa, ya jefar agaban Manzon Allah (saww) sannan yace:

"Na rantse da lata da uzza ba zan bada gaskiya gareka ba, har sai wannan yankakken damon yayi Imani dakai".

Sai Manzon Allah (saww) yace "YA KAI DAMO!!".

Sai Damon ya amsa acikin harshen larabci mai cike da fasaha. Dukkan mutane suna ji. Damon yace :
"LABBAIKA WA SA'ADAIKA YA KAI ADON DUKKAN MASU TARUWA ARANAR ALQIYAMAH!".

Sai Manzon Allah yace ma Damon "YA KAI DAMO, WA KAKE BAUTA MA?"

Sai Damon yace: "WANDA AL'ARSHINSA YAKE SAMA. MULKINSA YA MAMAYE QASA, HANYARSA TAKE CIKIN TEKU, RAHAMARSA TAKE CIKIN ALJANNAH, UQUBARSA TAKE CIKIN WUTA"

Sai Manzon Allah (saww) yace masa "NI KUMA WANENE, YA KAI DAMO?".

Sai Damon yace: "KAI NE MANZON UBANGIJIN TALIKAI, KUMA KAINE CIKAMAKIN ANNABAWA. DUK WANDA YA GASKATA-KA YA RABAUTA. WANDA YA QARYATA-KA KUMA YAYI ASARA."

Daga jn wannan sai Balaraben Qauyen nan yace: "Hakika wallahi nazo wajenka alokacin da adoron Qasa babu mutumin da nafi Qinsa fiye da kai. Amma ayanzu WALLAHI nafi sonka fiye da Iyayena da dukiyata, WALLAHI ina sonka ciki da waje, afili da boye.
- ASH'HADU AN LA'ILAHA ILLAL LAHU WA ANNAKA RASULULLAHI".

Nan take Balaraben kauye ya musulunta agaban Jama'a, kuma ya fara koyon karatun Alkur'ani awajen Manzon Allah (saww).

Bayan ya koma gida ta dalilinsa sai da Mutum dubu daga cikin Qabilarsa (banu sulaim) suka musulunta arana guda. kuma suka fito suka taya Manzon Allah (saww) Yaki akarkashin tutar KHALID BIN WALEED (RA).

Aduba Dala'ilun Nubuwwa na Abu Nu'aym shafi na 320.

Aduba ALBIDAYAH WAN NIHAYAH ta Ibnu katheer mujalladi na 6, shafi na 149.

Aduba KHASA'ISUL KUBRA na Suyuty mujalladi na 2 shafi na 65.

Sallu alaihi wa sallimu tasleeman.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (16-05-2017)

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI