LABARIN CIKIN QABARI
Ibnu Abid Dunya ya ruwaito ta hanyar Hammadu bn Salamah, shi kuma ya karbo daga Hisham bn 'Urwah, shi kuma daga Babansa yana cewa :
"Watarana wani mahayin doki yana tafiya atsakanin garin Makkah da Madeenah sai gashi kusa da wata Maqabarta, sai yaga wani mutum ya fito daga cikin Qabarinsa yana ci da Wuta!!. Ga kuma Qarafuna an daddaureshi dasu.
Sai yace "Ya kai bawan Allah! Hure min wutar nan! Hure min wutar nan!".
Nan take sai ga wani ya sake fitowa ta cikin wannan Qabarin, yabi wancan din yana cewa "Ya kai bawan Allah kada ka bushe masa (wutar nan)!"
Nan take shi wannan mahayin dokin ya suma akan dokin nasa. Kuma dokin yaci gaba da tafiya dashi ahaka har sai da ya kaishi wajen wata rijiya. Yayin da ya farka sai yaga duk gashin dake kansa ya juye ya zama furfura fari fat tamkar auduga!
Yaje ya bama Sayyiduna Uthman bn Affan (ra) labarin abinda ya faru (Zamanin Khalifancinsa ne). Sai shi Sayyiduna Uthman din ya hana mutum ya rika yin tafiya shi ka'dai.
Haka kuma Ibnu Abid dunya ya fidda wani hadithin ta hanyar Yahya bn Ayyub bn Alhad, shi kuma daga Muhammad bn Ibraheem, shi kuma Al Huwairith bn Rubaab (ra) yace :
"Watarana ina tafiya awani waje da ake kira Ithayah, sai ga wani mutum ya fito mana daga cikin wani Qabari, kansa da fuskarsa suna ci da wuta..
Kuma yana daddaure acikin wani sasari (chain) na baqin Qarfe. Sai yace mun "Shayar dani ruwa daga butar nan!".
Sai ga wani mutum ya fito shima daga Qabarin, yana binsa aguje yana ce mun "Kada ka shayar da kafiri".
Da ya tarar da wancan din sai ya danqi gefen wannan sasarin, ya fizgoshi da qarfi Ya kifar dashi akan fuskarsa sannan ya jashi har suka koma tare cikin Qabarin.
Sai Rakumar da nake kanta ta jani a guje, bana iya tsayar da ita (itama ta firgita). Har sai da ta iso wani waje cikin daji sannan ta tsaya na sauka na sallaci Maghribah da isha'i, Sannan na hau naci gaba da tafiya har sai da na wayi gari acikin Madeenah.
Yayin da naje wajen Umar bn Al-Khattab (ra) na bashi labarin abinda na gani, sai yace "Ya kai Huwairithu wallahi bana tuhumarka da Qarya. Amma labarin da ka bani din nan yana da tsanani sosai".
Sai Sayyiduna Umar ya aika aka taho da wasu dattijai daga Qauyukan dake kusa da inda abun ya faru, Kuma wadannan dattijan sun riski zamanin Jahiliyyah. Ya tambayesu game da abinda na bashi labari.
Yasa na maimaita musu labarin abinda na gani. Sai suka ce "Mun fahimci labarin Ya Sarkin Muminai!. Hakika Ma'abocin Qabarin nan wani mutum ne daga Banu Gifaar ya rasu tun zamanin Jahiliyyah".
Da Sayyiduna Umar yaji haka sai ya gode ma Allah, kuma yayi farin ciki kasancewar mutumin ya mutu ne tun zamanin Jahiliyyah din.
Da ya tambayesu ko menene halayen mutumin?. Sai suka ce "Shi dai wannan yana daga Mazajen Jahiliyyah wanda ya kasance ba ya kulawa da hakkokin baqo.
Hisham bn Ammar ya ruwaito acikin Kitabul Ba'athi daga Yahya bn Hamzah daga Nu'uman daga Mak'hool (rah) yace "Wani mutum yazo wajen Umar bn Al-Khattab (ra) duk kansa yayi furfura tare da rabin gemunsa. Sai Sayyiduna Umar yace masa "Menene ya sameka haka?".
Sai mutumin yace "Ya Sarkin Muminai! Hakika ni na wuce ta kusa da wata Maqabarta ne acikin wani dare. Sai naga wani mutum yana bin wani aguje, tare da bulalar wuta ahannunsa, duk sanda ya tarar da wancan din sai ya dakeshi da bulalar. Nan take ( sai naga ) Wutar ta kama jikinsa tun daga Qeyarsa har bayan sawayensa.
"Sai mutumin ya nemi gudunmuwa awajena, yace "Ya Kai Bawan Allah ka taimaka mun!".
Sai wancan dake binsa din yace "Ya kai bawan Allah kada ka taimakeshi. Hakika shi ba mutumin kirki bane!'.
Da Sayyiduna Umar yaji haka sai yace "Saboda irin wannan ne Annabinku (saww) ya hana mutum ya rika tafiya shi ka'dai".
Ya ku 'Yan uwa hakika azabar Qabari gaskiya ce. Kuma musabbabinta shine wulakantar da addini, rashin kulawa da tsarkin bawali, Annimimanci, gulma, wulakanta baqi, etc.
Allah shi kiyayemu. Ameen.
DAGA ZAUREN FIQHU (25-01-2018 07/05/1439).
Comments
Post a Comment