MADUBIN DUBAWA (70)

Yau madubin namu zai waiga baya ne ya dauko mana wani abu daga rayuwar magabatanmu wato tabi'ai da tabi'ut tabi'un.

Daga cikin magabata akwai wadanda tsoron wutar lahira da kuma tunaninta yasa suka haramta wa kansu yin dariya anan gidan duniya.

Isma'eel As-Suddiy (rah) yace "Lokacin da Hajjaju bn Yusuf (wani azzalumin gwamna ne) yasa aka kamo masa babban Malamin tabi'ai din nan mai suna Sa'eed bn Jubair kafin ya kasheshi sai ya tambayeshi cewa "Labari ya sameni cewa wai kai baka ta'ba yin dariya ba tunda kake!".

Sai Sa'eed bn Jubair (rah) yace masa "Ta yaya zan rika dariya alhali an riga an hura jahannama, Kuma Qukuman cikinta an riga an kakkafasu, Kuma Zabaniyawan cikinta an riga an tanadesu ? (Qukumi shine irin chain din da ake Qakaba musu a wuyansu lokacin da ake jibgarsu ana azabtar dasu. Zabaniyawa kuma sunan Mala'ikun nan ne Qarfafa guda goma sha tara wadanda Allah ya tanadar dasu domin azabtar da 'yan wuta).

Bayan Hajjaju ya kashe wannan Salihin bawan Allah, shi kuma nan take ya haukace bai warke ba har karshen rayuwarsa. Kuma dama ya gaya masa kafin ya kasheshi yace idan ka kasheni ba zaka sake iya kashe wani abayana ba.

Akwai wani Malami acikin magabata ana kiransa da Gazwaan, watarana yaje kashe gobara a gidan makobtansa sai wani garwashi ya sauka akan yatsansa har ya Qonashi sosai. Sai yace "Tunda naga wutar duniya ta qonani haka, wallahi ba za'a sake ganina ina dariya ba har sai ranar da na tabbatar shin Allah ya tseratar dani daga wutar Jahannama ne ko A'a!". Daga wannan ranar bai sake yin dariya ba har ya koma ga Allah!.

Hakika daga cikin magabata akwai wasu jama'a wadanda suka yiwa Allah alkawarin cewa ba zasu yi dariya ba har abada.. Sai sun san shin Aljannah ce makomarsu ko wuta!.

Acikinsu akwai Jum'atud Dausiy, da Rabee'u bn Khurash da dan uwansa Rub'ee bn Khurash, da Aslam Al Ijlee, da Wuhaibu bn Wardi, da wasunsu masu yawa.

Yazeedur Raqqashee ya ruwaito hadisi daga Sayyiduna Anas bn Malik (Allah ya yarda dashi) yace "Yayin da akayi Isra'i da Manzon Allah (saww) yana tare da Mala'ika Jibreelu (alaihis salam) sai ya ji wata Qara. Sai  yace "Wacce irin Qara ce wannan Ya Jibreelu?".

Sai Mala'ika Jibreelu yace "Wani dutse ne wanda Allah ya jefashi daga bakin ga'bar Jahannama tun shekaru saba'in yana ta wulwulawa acikinta sai yanzu ya kai Qasanta".

Tun daga wannan ranar Manzon Allah (saww) bai sake yin dariya ba har ya bar duniya. sai dai murmushi.

Akwai wani dogon hadisi na Abu Dharrin Al Ghifariy (radhiyallahu anhu) wanda acikinsa ya tambayi Manzon Allah (saww) cewa "Ya Rasulallahi shin menene acikin Suhufi Musa? (wato litattafan Annabi Musa alaihis salam).

Sai Manzon Allah (saww) yace "Ta kasance duk cikinta misalai ne (Kama) "Ina mamakin wanda ya tabbatar da mutuwa gaskiya ce, amma yake farin ciki. Ina mamakin wanda ya tabbatar da cewa Wutar lahira gaskiya ce amma yake dariya.."

(Ibnu Hibban ne ya riwaito hadisin).

Dole ne takaici ya lullubeka idan ka dubi rayuwar irin wadannan magabatan sannan ka kalli irin dimaucewar da mukayi awannan zamanin namu wajen neman duniya ta kowanne hali.

Ga yawan ayyukan sa'bo, ga Qarancin tuba. Ga yawan dogon buri, ga kuma Qarancin biyayya ga Allah. Ga yawaitar ilimi da kafofin sadarwa, amma ga Qarancin aiki da ilimin. Ga son jin dadi ga Qarancin tsoron Allah!!!.

Ya Allah tuba mukeyi ka gafarta mana kada ka kamamu idan mukayi mantuwa ko kuskure. Kada ka dora mana nauye-nauye kamar yadda ka dora ma wadanda suka gabacemu. Ya Ubangijinmu kada ka ka dora mana abinda ba zamu iya ba. Kayi muna rangwame ka gafarta mana, kaji Qanmu Kaine majibincinmu,  ka taimakemu akan kafiran mutane da azzalumai. Ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (13/04/2019  06/08/1440)

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI