RANAR RABON TAKARDU!!!
Ranar da za'ayi rabon takardu, rana ce wacce hankula ke tashi.. Idanuwa suna kuka amma babu zubar hawaye...!
Mutane zasu kasance kaso uku ne awannan lokacin :
# Akwai wadanda ba za'a basu littafi ba. Wato ba za'a yi musu hisabi ba. Kamar Annabawa kenan (as) da manyan Salihan bayin Allah da Siddiqai da Shahidai.
# Akwai wadanda zasu karbi littafinsu ta hannun dama. Sune wadanda za'ayi musu hisabi sassauka. Wato ba za'a duba laifukansu ba.
Farkon wanda zai karbi Littafinsa da hannun dama shine Sayyiduna Umar bn Khattab (rta). Kamar yadda hadisi ya fada.
# Akwai wadanda zasu karbi littafinsu ta hannun haggu. Acikin wata ayar ma Allah yace zasu karba ne ta baya.
Wato Mala'iku zasu sanya hannunsu na hagu su fasa musu Qirjinsu dashi, sannan su zaroshi ta baya, Sannan a miko musu littafin nasu.
Za'a ce ma kowanne daga cikinsu "KARANTA LITTAFINKA DA KANKA.... "
A sannan ne Dan Adam zai tuno da dukkan abinda ya aikata a rayuwarsa ta duniya.. Wato dukkan kalmomin da harshensa ya furta na alkhairi ko sharri..
Tare da duk wani aikin da ya ta'ba aikatawa da hannunsa ko Qafarsa ko al'aurarsa..
Masu laifi zasu fara yin jayayya suna musanta abinda suka gani acikin litattafan ayyukansu. Zasu rika cewa :
"YA KAITONMU! WANNE IRIN LITTAFI NE WANNAN?! BA YA BARIN WANI QARAMIN ABU KO BABBA FACHE SAI YA KIDIDDIGESHI!".
Ubangiji zai yi umurni akawo MIZANIN AUNA AYYUKAN BAYIN ALLAH... (SUBHANALLAH). Wallahi hatta Mala'iku idan suka kali Mizanin nan sai hankalinsu ya tashi... Saboda tsananin girmansa.
Wallahi koda rubutun nan da kake karantawa yanzu, awannan ranar sai kaga labarin karantawar nan da kayi tare da kwanan wata da lokaci, ajikin wannan littafin..
Zasu ce "TSARKI YA TABBATA GAREKA YA UBANGIJINMU! SHIN WANNAN ME ZA'AYI DASHI!...
Babu wani wanda aka zalunta aduniya fache sai Ubangiji ya karbar masa hakkinsa daga wanda ya zalunceshi... Koda tsakanin 'Da da Uba, ko Miji da Mata, ko Dan uwa da Dan uwa, ko aboki da aboki...
LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYYIL AZEEM!!!
Ya Allah hakika na tabbata babu wajen gudu, babu matsera ko Mafaka daga gareka sai zuwa gareka...
Ya Allah ka gafarta mana tare da mahaifanmu. Ka sanyamu cikin wadanda zasu shiga Aljannah ba tare da hisabi ko Uqubah ba. Ameeen.
DAGA ZAUREN FIQHU (22-11-2016).
Comments
Post a Comment