MADUBIN DUBAWA (64)
Sa'eed bn Sulaiman yace "Na kasance acikin garin Makkah tare da Abdullahi bn AbdilAzeez Al Umariy ('Daya daga cikin Maluman Tabi'ai masu gudun duniya). Alokacin nan Khalifah Harunar Rasheed yazo wajen aikin hajji. Sai wani mutum yace wa Abdullahi Al Umariy, "Ya kai baban Abdurrahman! Gashi chan Sarkin Muminai (Harunar Rasheed) yana Sa'ayi (wato tafiya tsakanin Safa da Marwah) kuma duk an bar masa wajen sa'ayin!". Sai shi Abdullahi Al Umariy din yace ma mutumin "Kada Allah ya saka maka da alkhairi domin ka dora min wani aiki wanda na wadatu da barinsa". Sai ya tashi ya dauki takalmansa ni kuwa ina binsa abaya. Sai ga Harunar Rasheed ya taho daga Marwah ya nufi Safaah.. Sai Abdullahi Al Umariy yayi kiransa yace "YA KAI HAROON!". Da khalifan ya waiwayo ya ganshi sai yace "Amsawarka Ya baffana!". Sai yace "Mu hau dutsen Safaa". Yayin da suka hau sai yace ma Khalifan "Sanya idanuwanka wajen 'Dakin All