MATSALAR CIN HANCI A NIGERIA

Shekaru biyu da suka wuce naje Qasar Togo sannan na wuce Kamaru (Cameroun) kuma na shiga airport na kowacce Qasa. Amma har naje na dawo babu inda aka tambayeni "NA-GORO" sai anan Nigeria.

Kuma abun kunya ma a international airport dinmu na Lagos nan ne abun yafi Qamari. Ba sani ba sabo, idan kazo babu "Yellow card" sai ka sayeshi akan Naira dubu uku ko hudu (abun naira 300) in ba haka ba, ba zaka wuce ba.

Haka ma Ma'aikatan dake duba passport din matafiya, sai sun tambayeka "NA GORO" kafin ka wuce ta gaban teburinsu.

Duk wanda ya shigo Nigeria daga Nijar ta kan bodar Illela ko Kongolam zai baka labarin irin cin zarafin da ma'aikatan Nigeria suke yiwa 'Yan Qasar Nijar (Abun tausayi wallahi).

Ga Misali : Duk lokacin da zasu shigo Qasar nan sai Ma'aikatan sun leka cikin motocin sun kirge adadinsu. Kuma kowannensu sai ya bayar da ₦200 in ba haka ba, sai dai ya koma Qasarsa.

  Sannan idan sunzo Kano sunyi sayayyar kaya, akan hanyar komawarsu Qasarsu sai sun sake biyan (₦200) a kowanne GATE din Ma'aikatan Nigeria. Kuma gates din nan sun kai guda uku ko hudu akan hanyar.

Abun haushin ma shine wannan sun mayar da karbar haram din nan tamkar halal dinsu. Duk da cewa mafiya yawansu Musulmai ne kuma 'Yan Nijar dinma Musulmai ne, kuma karbar kudin nan ya sa'ba ma dokar Allah da Manzonsa (saww) kuma ya sa'ba ma dokar Nigeria, balle dokar Qasa da Qasa ko dokar 'Yancin Dan Adam.

Fatanmu dai Allah ya kawo gyara, Allah ya shiryi masu yi ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (03/09/2018)).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI