FA‹IDODIN SALATIN ANNABI (SAWW) DAGA ZAUREN FIQHU (KASHI NA FARKO

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Tsira da aminci su tabbata ga Annabin da Allah ya aikoshi domin rahama ga dukkan Talikai, tare da iyalan gidansa da dukkan Sahabbai da bayin Allah Salihai.

Salatin Annabi (saww) wata irin ibadah ce wacce babu irinta acikin dukkan ibadun da Mumini zai iya yi da harshensa.

Tana kunshe da falala wacce 'Dan Adam ba zai san iyakarta ba. Domin ita wata babbar hanya ce wacce take nuna jin Ƙai irin na Allah ga bayinsa.

Malamai da yawa sunyi rubuce rubuce akan sha'anin Salatin Annabi (saww) Musamman bangaren falalarta da kaifiyyoyinta.

Acikin littafinsa mai suna "KHULASATUL ADILLATISH SHAR'IYYAH FIR RADDI 'ALA TASA'ULATIL HASHAWIYYAH, Babban Malamin nan Muhammad Miftah bn Salih ya kawo fa'idodin Salatin Annabi (saww) har guda Sittin da biyar (65). Amma guda arba'in ya cirosu ne daga littafin Ibnul Qayyim Al-Jawziyyah mai suna JILA'UL AFHAAM FIS SALATI WAS SALAM 'ALA KHAIRIL ANAAM, shafi na 129-135.

Ga fa'idodin nan kamar haka:

1. Cika umurnin Allah ne (SWT). Tunda shi ya gayyaci Muminai cewa suyi salati ga wannan Annabin mai girma (saww).

2. Yin Muwafaƙah da Allah (SWT). wato yin irin abinda Allah ma yana yinsa.

3. Yin Muwafaƙah da Mala'ikunsa (as) tunda su ma suna yin Salati agareshi (saww).

4. Ana daukaka darajar mutum har sau goma, saboda salati guda 'daya Tal wanda yayi ma Shugaba (saww).

5. Za'a rubuta maka kyawawan lada har guda goma, Ta dalilin Salati guda 'daya tal!.

6. Allah da kansa zai maka salatai guda goma irin nasa (SWT).

7. Za'a kankare maka laifuka guda goma.

8. Za'a amshi dukkan abinda ka roƙa bayan Salati ga Manzon Allah (saww).

9. Dalili ne na samun ceton Manzon Allah (saww) idan kayi salatin shi kadai ko kuma ka hada da neman Waseelah ga Manzon Allah (saww).

10. Dalilin samun gafara ne daga Allah (swt).

11. Shi Salatin Annabi (saww) babbar hanya ce ta samun isarwar Allah gareka akan dukkan abinda ya dameka (wato Allah zai share maka hawayenka).

12. Salatin Annabi (saww) hanya ce ta samun kusanci ga Manzon Allah (saww) aranar Alqiyamah.

13. Idan kayi salati agareshi (saww) to Allah zai baka ladan wanda yayi sadaqah. (Musamman ga Matalauta).

14. Hanya ce ta samun biyan bukatu cikin Sauki in sha Allahu.

15. Hanya ce ta samun Salatin Mala'iku agareka da zarar kayi masa (saww).

16. Hanya ce ta samun tsarkakuwar zuciyar mai yin salatin.

17. Hanya ce ta samun bisharar samun Aljannah agareka tun kafin mutuwarka.

18. Hanya ce ta samun tsira daga tashe-tashen hankulan ranar Alqiyamah.

19. Hanya ce ta samun mayar da salati da sallama agareka daga Annabi (saww).

20. Hanya ce ta samun tunawa da abinda ka manta (Wato idan ka manta da wani abu, da zarar kayi ma Annabi salati sai kaji ka tuno da abun).

21. Hanya ce ta samun Qamshib wajen Zama, kuma duk wajen zaman da akayi ma Annabi salati, ba zai zama abin nadama ga Ma'abotansa ba, aranar Alqiyamah.

22. Ta dalilin yin salati agareshi za'a cire sunanka daga layin Marowata awajen Allah.

23. Ita hanyar tsira ne ga mai yinta, Domin Allah zai kirashi da bawansa.

24. Ita hanya ce ta samun kuɓuta daga turmuzuwar hanci ga wanda bai yi salati agareshi ba, duk sanda aka ambaceshi.

25. Salatin Annabi (saww) yana sanya mai yinsa akan Tafarkin shiga Aljannah. Kamar yadda kuma duk wanda ba ya yinsa ya kauce ma hanyar Aljannah.

Anan zamu tsaya, sai akaratu na gaba in sha Allahu zamu ɗora daga nan inda muka tsaya.

Salati da aminci su tabbata agareka Ya Abal Qasimi, gwargwadon darajarka da matsayinka awajen Ubangijinka.

Albarkacin wannan salatin ya Allah ka tabbatar damu bisa tafarkinka madaidaici, tare da 'Ya'yanmu da dukkan iyalanmu.

AN GABATAR DA KARATUN  NE A ZAUREN FIQHU WHATSAPP -3 RANAR 10-06-2016 (05-09-1437).

Barkan mu da shan ruwa

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR SAMUN BIYAN BUKATU