MAI DADIN SUNAYE (SALLAL LAHU ALAIHI WA ALIHI WA SALLAM (10)

Da Sunan Allah Makadaicin da bashi abokin tarayya.. Salati da aminci mafiya cika da martaba su tabbata bisa Cikakken Bawan Allah, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa masu alfarma, tare da dukkan Magabata na kwarai da waliyyan Allah da dukkan nagartattun bayinsa.

Wannan shine karo na goma (10) acikin darasin Zauren Fiqhu wanda acikinsa muke yin sharhi tare da bayanai takaitattu game da ma'anonin wasu daga sunayen Shugaban mutanen farko da karshe (Sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

17. SAYYIDUN : WATO SHUGABA (SAWW). Shine Shugaban halittun farko da Karshe. Tun daga kan Banu Adam har Mala'iku da Aljanu da dabbobi da dukkan abinda ke karkashin wannan Ma'anar.

Acikin hadisin da Imamul Bukhariy ya ruwaito, Manzon Allah (saww) yace "NINE SHUGABAN 'YA'YAN ADAM ARANAR ALQIYAMAH, KUMA BA ALFAHARI NAKEYI BA".

Kuma yace "NINE MAFI GIRMA AWAJEN UBANGIJINA ARANAR ALQIYAMAH".
(Riwayar Tabaraniy).

Kuma yace "ADAMU DA DUK WANDA KE QASANSA SUNA KARKASHIN TUTANA ARANAR ALQIYAMAH".

Shi keda dukkan Matsayai da Muqamai na girma. Babu wanda ya kaishi balle ya fishi acikin dukkan bayin Allah. Anan duniya babu yashi, balle kuma aranar Alqiyamah.

Shine farkon tashi awannan ranar. Kuma shine farkon wanda zai yi magana da Allah (SWT). Maqamul Mahmudi nasa ne. Shafa'atul Uzma tasa ce.. Liwa'ul Hamdi (Tutar godiya) tana hannunsa. Shi keda ceton farko da na Karshe, kuma shi keda mabudin komai awanann ranar.

18. SIRAJUN : FITILAR HALITTU (SAWW). Hakika Annabi Muhammadu (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) shine fitilar halittu baki daya. Domin shi yazo da hujjoji bayyanannu wadanda dasu mutum ke iya rarrabewa tsakanin Qarya da gaskiya, tsakanin shiriya da 'bata, tsakanin ilimi da jahilci.

19. MUNEERUN : (MAI HASKAWA) Shine ya haskaka ma muminai suka gane hanyar gaskiya suka bita kuma suka rabauta. Kuma acikin haskensa suka samu dukkan abin nema.

Su kuwa kafirai ya nuna musu hanyar gaskiya ama basu bita ba, sai suka zabi bin kishiyarta. Don haka suka 'bata, kuma Qarshen tafiyarsu ita Wuta wacce zasu dawwama acikinta har abada.

Allah Madaukakin Sarki yace masa "YA KAI WANNAN ANNABI! HAKIKA MU MUN AIKETA AMATSAYIN MAI SHAIDAWA, KUMA MAI YIN BISHARA, KUMA MAI GARGADI. KUMA MAI KIRA ZUWA GA ALLAH DA IZININSA, KUMA FITILA MAI MAI HASKAKAWA".

Anan zamu tsaya da fatan Allah shi Qara mana So da Qauna da ladabi da biyayya da ganin girman Manzonsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

In sha Allahu akwai darasin Zauren Fiqhu yana nan tafe mai taken "MU SAN ANNABINMU" wanda acikinsa zamu rika kawo muku ire-iren abubuwan dake da alaqah da Ma'aiki (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

An gabatar da karatun a Zauren Fiqhu Whatsapp (3) ranar 03/04/2018.

© ZAUREN FIQHU ISLAMIC FOUNDATION.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI