MUMMUNAN ZATO

Mummunan zato yana daga cikin manyan kaba'irori da Allah ya haramta. Idan mutum ya zamanto mai yawan yiwa jama'a mummunan zato, da sannu sai ya mayar da masoyansa sun zamto makiyansa..

Da sannu zai zamanto Azzalumi kuma magulmaci.. Zai zalunci musulmai wajen yi musu yarfe da Qage da Qazafi. Kuma duk suna daga cikin manyan zunubai..

Watarana zai iya yin zancensu awajen wasu, yace wane yayi mun kaza da kaza, wane bai kyauta mun ba.. Alhali kuma ba lallai ne hakan ya zamto gaskiya ba.

Daga cikin hakkokin da kowanne Musulmi yake dashi akan 'yan uwansa Musulmai, akwai cewa "KADA AYI MASA ZATO SAI NA ALKHAIRI" Sai dai idan ya aikata abinda ya keta alfarmar shari'a, to anan kuma Jama'ar musulmai suna da damar yin Qararsa, kuma shari'a tana da damar yin bincike kafin yanke hukunci akansa.

Kyautata zato ga 'yan uwa da makusanta da masoya, yakan kawo hutun zuciya da sulhu da hadin kai atsakanin juna. Bayan kuma dimbin ladan dake cikin yin haka.

Amma shi mummunan zato yakan janyo saurin 'batawa da yankewar igiyar zumunci tare da daukar hakkin mutum ba tare da saninsa ko laifinsa ba.

Wani daga cikin magabata yace "Koda wani abu ya bayyana daga dan uwanka musulmi, to yi kokari ka nema masa mafita ta alkhairi har sau saba'in kafin kayi masa mummunan zato".

Mummunan zato yana taka mummunar rawa wajen kawo lalacewar aurarraki tare da lalata zamantakewar ma'aurata. Kuma wannan yana da mummunan tasiri wajen ginuwar kyakkyawar tarbiyyah ga yara masu tasowa.

Daga cikin misalan da zan iya bayarwa, mu dauki kamar matan dake leken wayoyin mazajensu, su shiga contacts su shiga messages na SMS da Whatsapp, alamar mummunan zaton da suke yiwa mazajensu ne. Sho ya janyo haka.

Yanzu wa zai iya Qidaya yawan matan auren da suka zamo zaurawa ta dalilin leken wayar Miji?. Wa zai iya Qidaya wadanda suka kamu da chutar hawan jini ta dalilim bakin cikin abinda suka gano awayoyin mazajensu?.

Wa zai iya fa'dar adadin budurwar da Matar aure ta kirata awaya ta zagi iyayenta, tayi mata Qazafin zina ko karuwanci, don kawai taga wasikarta awayar mijinta?.

Idan ka ajiye kyakkyawan zato azuciyarka, koda mutum yayi ma laifi,  koda da niyyah yayi, ba zaka zata masa komai ba, sai alkhairi.

Ajiye miyagun abu azuciya game da mutum shi kesa nan da nan da zarar abu ya bayyana komai kankantarsa sai ya zama babba.

Wallahi ya zama wajibi jama'a mu rika kyautata zatonmu ga junanmu. Zamu fi samun zaman lafiya da hadin kai da kwanciyar hankalin. Allah yasa mu dace.

Wannan nasiha ce daga Zauren Fiqhu 07064213990 {18/09/2018 08/01/1440).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI