Posts

Showing posts from March, 2016

RANAR DA BABU KOKWANTO

Image
'Dora hannunka akan Qirjinka... Zakaji yadda zuciyarka take bugawa, babu dare babu rana.. tana tafiya ne bisa wani Saiti na musamman wanda Ubangijinka yayi mata tun asali. Nisan tafiyar wannan saitin shine Gwargwadon nisan ajalinka. Kuma Ubangijinka yana sane da yawan adadin bugawar da yayi izini agareta. Idan lokacinta ya cika, ba zata jinkirta maka ba, Ba zata Qara motsi ba. Ranar da Mala'ikan numfashinka da Mala'ikan abincinka, da Mala'ikan abin shanka zasu zo suyi bankwana dakai, suce maka dukkan rabonka na duniyar nan ya riga ya Qare. Ranar da Iyayenka da 'Yan uwanka da iyalanka zasu kewayeka, amma ba zasu amfana maka komai ba... Ba zasu hana abinda zai sameka ya sameka ba, kuma ba zasu sanya ajinkirta maka ba, kuma ba zasu sanya a saukaka maka ba. Wallahi duk wannan kururuwar da sukeyi TA QARYA CE! Suna yin kuka ne don tsoron halin da zasu shiga bayan rasuwarka. Amma ba wai sunayi ne domin tausaya maka akan halin da zaka shiga ba.. Kuma WALLAHI duk cikin

HANYOYIN RABUWA DA MASTURBATION

Hakika matsalar Istimna'i (wato Masturbation) gagarumar matsala ce wacce take shiga zuciyar masu yinta, tayi KAKA-GIDA. Kuma tana da wahalar fita gaba dayanta dole sai dai albarkacin addu'a da kuma yawaita ibada mutum zai samu wadatuwar tsoron Allah azuciyarsa harma ya zamto ba zai iya aikatawa ba. Mafiya yawan samari suna yi ne bisa niyyar wai zasu kauce ma ZINA. Basu san cewa shima wannan din babban Kaba'ira bane!! Matasa Maza da Mata da dama sun afka cikin wannan bala'in. Wasu cikin rashin sanin illolinsa, wasu kuma saboda tsabar Fajirci. Kuma kamar yadda zina take da mutukar Illa tana cutar da lafiyar mutum, ta chutar da hankalinsa, da gurbata tunaninsa, ta cire masa Kwayar Imani da tsoron Allah daga zuciyarsa, to hakanan shima Istimna'i yake lalata rayuwar mutum da mutuncinsa da lafiyarsa. Lallai wajibi ne ga duk mutumin da yake son kansa da arziki, kuma yake fatan gamuwa da Allah lafiya, ya nisanci Zina da dangoginta irin su Luwadi, Madigo, Istimna'i,

MAGANIN CIWON SUGAR (DIABATES)

MAGANIN CIWON SUGAR (DIABATES) TAMBAYA TA 1893 ******************** Assalamu alaikum malam, na kasance Ina fama da matsalar ciwon siga, Ina yawan jin kishirwa domin nakan sha pure water guda uku, sannan nakanyi fitsari sau biyar cikin dare. kadan ne bai cika robar fenti ba amma yanzu dana sha wani maganin asibiti ya sassauta nakan tashi sau biyu, kuma bana jin komi ajikina amma wani sa,in nakanji babbar yatsar kafana ya rike yayi tsami, sannan idona sai nayi nesa da waya nake gani,sannan yana kara ramar dani.Dan Allah malam a taimaka min da magunguna na musulunci DA zan yi amfani dasu domin samun lafiyata. daga wata baiwar Allah. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Acikin magungunan Musulunci babu abinda ke magance matsalar ciwon Sugar (Diabates) fiye da Hulbah (Fenugreek). Tana kunshe da sinadarin Insulin wanda ke taimakawa wajen samar wa Jikin majinyacin abinda yake bukata. Don haka ki nemi garin Hulba cokali 7, garin Zaitun Cokali 7, Garin Fijil Cok

TAMBAYA AKAN HUKUNCIN KARBAR KUDIN BIKI

HUKUNCIN KARBAR KYAUTUKA RANAR BIKI TAMBAYA TA 1892 ******************** Assalam Alaikum Warahmatullah. Malam Allah Yasaka da Alkhairi Ya kuma Biya da Gidan Aljanna. Malam Ina Da Wadansu Yan Tambayoyi Da fatan Allah Zai Bada Ikon Amsawa Ameeen. 1. Malam Dan Allah Menene Hukuncin Biki A Musulunci Ina Nufi Kamar yadda Mata Suke yi. Har ma da Wasu Mazan Za kaga Idan Abun Alheri Ya samu Mutum Kamar Bikin Suna Ko Bikin Aure. To Zaka ga An Kaiwa Mutum Kudi. idan Na kaiwa Mutum 2000 Shi kuma Idan Ya tashi Zai Kawo mun 4000 To Malam Haka Ya Halatta? 2. Malam shin ya dace Mutum Yayi ma Mutum HAPPY BIRTHDAY. Kaman A Social Media Zaka ga Mutane Suna Turama Junansu Birthday Wishes. 3. Malam Menene SUJUDUSH SHUKUR? Ya Kuma Akeyinta? Kuma Wanda Daliline Yasa Akeyi? Nagode Allah Yasaka da Alkhairi Daga Dalibinka. AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Eh ya halatta idan wani abun murna ya samu 'dan uwanka, kamar aure, ko haihuwa kayi masa wani abu na kyautataw

FADAKARWA MAI GIRMA

Image
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM Abut Tufayl (ra) ya bada labari cewa Azamanin Annabi (saww) akwai wani mutum wanda aka haifa masa yaro. Sai ya daukoshi ya kawo wajen Manzon Allah (saww). Sai Annabi (saww) ya karbeshi ya sanya hannunsa mai albarka akan goshinsa. Nan take sai wani irin gashi mai mutukar kyawu kamar gashin wuyan doki ya tsiro akan goshin yaron. Har yaron ya girma gashin yana nan. To lokacin da Khawarij suka fito, sai wannan yaron yabi irin ra'ayinsu. Sai gashin nan ya zube daga goshinsa. Mahaifin nasa da yaga haka sai ya kamashi ya kulleshi agida, ya hanashi fita don kar ya koma wajensu. Abut Tufayl yace sai muka shiga wajensa mukayi masa wa'azi muka ce masa "Shin yanzu baka ganin albarkar Manzon Allah (saww) wacce take tare dakai gashi nan ta Zube?". Bamu gushe ba, muna yi masa wa'azi har sai da ya tuba ya dawo daga kan ra'ayinsu. Sai Allah ya dawo masa da wannan gashin akan goshinsa tunda ya tuba. Wannan Mu'ujiza ce mai girma daga Sayyi

ADDU'A DAGA BAWAN ALLAH MAI RAUNI ZUWA GA UBANGIJINSA MAI JIBINTAR LAMARINSA

Ya Allah Ya Ubangijin Jibreelu da Mika'ilu da Israfeel!! Ya Ubangijin Annabi Ibraheem da Annabi Isma'eelu da Annabi Is'haqa da Annabi Musa da Annabi Eisa (as)!! Ya Ubangijin Annabi Muhammadu (saww).. Ya Masoyin Annabi Muhammadu (saww). Ya Masoyin bayinsa masu Ikhlaasi! Ya Mafi Jin-Qan Masu Jin-Qai, Ya Mafi Tausayin Gajiyayyu!! Ya Mai taimakon Raunana!! Ya Mai amsa rokon masu Roko!! Ya mai bayarwa ba tare da lissafi ba! Ya mai yafewa ba tare da ba tare da Hisabi ba!! Ya Allah muna godiya gareka bisa dukkan Ni'imomin da kayi mana afili da boye. Wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba. Hakika Kai mai yawan kyauta ne ga bayinka. Ya Allah ka gafarta Zunubanmu, ka shafe kusakurenmu, Ka Warkas da Zukatanmu masu Jinya, Ka 'dora karayar Jikkunanmu. Ka shayar da Qishirwarmu, ka Qosar da yunwarmu. Ka Suturta tsaraicinmu. Ka rufa asiranmu, Ka Qarfafi rauninmu! Ya Allaah ka albarkaci rayuwarmu, Ka shirya dukkan Zuriyarmu, Ka ilmantar damu daga Jahilci. ka raya zukatanm

NASIHA NASIHA NASIHA

Kowanne mutum yana yin kyauta ne da irin dukiyar gidansu. Don haka idan Mutum ya jefo maka Baqar magana ko ya zageka, Shi irin kayan gidansu kenan. Kai kuma yi Qokari ka danne fushinka ka mayar masa da kyakkawa ko kuma kayi shuru ka kyaleshi. Yin afuwa ga wanda ya chucheka musamman alokacin da kake da ikon ramawa ko daukar mataki akansa, Ba Qaramin abu bane. Manzon Allah (saww) yace "Duk wanda ya danne wani fushi alhali yana da ikon zartar dashi, to aranar Alqiyamah Allah zai yi kiransa agaban dukkan halittu yace masa "SHIGA ALJANNAH DUK TA INDA KASO". Babu wata ribar da zaka ci idan kayi jayayya ko Musu ko ramukon zagi ko cin mutunci. Amma lallai riba mai yawa tana tare dakai alokacin da kayi shuru ka danne fushinka. Allah yasa mu gane. DAGA ZAUREN FIQHU (02-03-2016).

HANYOYIN SHIGA ALJANNAH (025)

HANYOYIN SHIGA ALJANNAH (025) TAUHEEDI DA IKHLASI *********************** Hadisi daga Sayyiduna Abdullahi bn Mas'ud (ra) yace: "DUK WANDA YA MUTU BA YA YIN SHIRKA GA ALLAH, TO ZAI SHIGA ALJANNAH". # Muslim ne ya ruwaito hadisin. aduba Tafsirin Ibnu Katheer juzu'i na 2 shafi na 189. BAYANI ******** Tawheedi shine babban dalili ko kuma hanya, ko kuma shaida (Ticket) wanda yake lamunce ma mutum samun duk wata alfarma alahira. Babu wanda zai samu damar yin cheto, ko kuma samun cheto awajen Allah ko Annabinsa (saww) ko Sahabbai ko Mala'iku ko Salihan bayin Allah sai wanda ya mutu da Imani. Don haka ya kamata mu nemi ilimi mu san shin menene Imani, Kuma yaya ake Ingantashi, kuma menene yake warwareshi! Domin Wallahi Mumini bashi da wata kadara mai tsada agareshi fiye da Imaninsa. Shi dai imani, Qudiri ne azuciya, da Furuci a baki, da kuma ayyuka na gabobi. Imani yana Qaruwa ta hanyar yawaita ayyukan alkhairi. kuma yana raguwa ta hanyar yawaita sa'bon All

MAGANIN KAIKAYIN GABA

MAGANIN KAIKAYIN GABA TAMBAYA TA 1876 ******************** Ass. Mallam ya dawainiya da jamaa Allah yajikan iyaye amen. 1.Matata ce take fama da kaikayin gaba ataimaka mana da Magani. 2. Maganin karfin mazakuta saboda shekaruna basuwuce talatinba amma idan ina jimai daga naje sau daya sai innakoma a Karo nabiyu sai gabana ya mutu. Ataimaka mana da magani nagode. Daga U. Abdullah. AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Shi kaikayin gaba yana da dalilai da suke kawoshi. Idan ba'a magance ainahin dalilin ba, to gaskiya za'a dade ana shan magani amma ba za'a samu nasara sosai ba. Idan tana da Jinnul Ashiq (Aljanin soyayya) wanda ke zuwa yana saduwa da ita, to lallai zatayi fama da Qaikayin gaba. Kuma ba ya jin magani har sai an magance ainahin aljanin dake tare da ita tukunna. Idan kuma wata chuta ce wacce ake dauka ta hanyar Jima'i, to shima sai an maganceshi kafin Kaikayin ya dena. - Ta nemi garin Hulba cokali 2, garin Magarya shi kuma co

FALALAR RAKA'ATAYIL FAJRI

Raka'atayil Fajri : Sune raka'o'in nan guda biyu na nafila wadanda ake yi bayan Hudowar Alfijir, kafin sallar Asubahi. Wannan sallar tana da inganci sosai. Domin Annabi (saww) ya bata muhimmanci. Ya kasance yana yinta aduk halin da yake ciki. Koda awajen tafiya, ko azaman gida. Nana A'ishah (rta) ta ruwaito cewa Annabi (saww) ya kasance yana karanta Fatiha ne kadai acikinta. KUMA tana yinta ne aboye. (wato yana yin karatunta a sirrance). Daga cikin falalarta, Sayyiduna Abdullahi bn Umar (rta) ya ruwaito cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) cewa : "Ya Rasulallahi ina so ka nuna min wani aiki wanda Allah zai amfanar Dani saboda shi". Sai Annabi (saww) yace masa "KA KULA DA RAKA'ATAYIL FAJRI DOMIN ACIKINTA AKWAI FIFIKO (WATO FALALA)". (Tabaraniy ne ya ruwaitoshi). Acikin wata ruwayar kuma Abdullahi bn Umar (ra) yace "Naji Manzon Allah (saww) yana cewa : "KAR KU BAR YIN RAKA'O'IN

KU DUBA WANNAN GIRMA!!

KU DUBI WANNAN GIRMA! *************************** Sayyiduna Abu Hurairah (ra) yace "Watarana muna sallar Isha'i tare da Manzon Allah (saww). Idan yayi Sujadah sai Al-Hasan da Al-Husain (ra) suyi tsalle su hau kan bayansa. Idan zai dago kansa, dai ya sanya hannunsa ya rikesu ta bayansa ahankali, ya saukesu daga kan bayansa. Kuma idan ya sake (yin Sujadar) sai su komo. (Wato su sake hawa bayansa). Har sai da ya idar sai sallarsa dai ya darasi bisa chinyarsa. Sayyiduna Abu Hurairah yace: "Ya Rasulallahi shin in mayar dasu ne?" (wajen mahaifiyarsu?). Nan take sai wata Walkiya ta hasko wajen. Sai Manzon Allah (saww) yace musu "KU TAFI WAJEN MAHAIFIYARKU". Walkiyar nan bata bace ba, taci gaba da haska musu hanya. Har sai da suka shigo wajen Mahaifiyarsu (Tsira da amincin Allah gareta da Mahaifinta). Acikin wata ruwayar kuma Abu Hurairah (ra) yace : "Al-Hasan (ra) ya kasance awajen Manzon Allah (saww) acikin wani dare mai tsananin duhu. Kuma Manzon A

KAR KA DAMU DA MASU HASSADA

Kar ka damu da hassadar masu hassada. Wannan ba zata Cuceka ba, mutukar ka rike Allah. Shi Allah din zai isar maka. Daga lokacin da ka fahimci cewa wane ba ya Qaunarka, ko kuma wane yana yi maka hassada, to kar ka Qishi. Kar ka rama abinda yake yi ma. Ka sani cewa kyautatawa zuwa ga masu yi maka hassada, yana Qara maka daukakar daraja ne awajen Allah. Sannan kuma yin hakan zai zama garkuwa gareka daga sharrinsu. Ita hassada guba ce wacce take saurin hallakar da masu yinta, tun kafin ta shafi wanda akayi dominsa. Don haka idan ka kyale Mahassada da halinsu, sharrinsu ma ya ishesu bala'i. Shi yasa Allah ya umurci Annabinsa (saww) cewa ya nemi tsari daga sharrin Mai Hassada yayin da yake hassadarsa. Ya Allah ka kiyayemu daga sharrin mahassada da matsafa da miyagu albarkacin hasken Alqur'aninka. Aaameeen. DAGA ZAUREN FIQHU (01-03-2016).