MAGANIN CIWON SUGAR (DIABATES)

MAGANIN CIWON SUGAR (DIABATES)

TAMBAYA TA 1893
********************
Assalamu alaikum malam, na kasance Ina fama da matsalar ciwon siga, Ina yawan jin kishirwa domin nakan sha pure water guda uku, sannan nakanyi fitsari sau biyar cikin dare. kadan ne bai cika robar fenti ba amma yanzu dana sha wani maganin asibiti ya sassauta nakan tashi sau biyu, kuma bana jin komi ajikina amma wani sa,in nakanji babbar yatsar kafana ya rike yayi tsami, sannan idona sai nayi nesa da waya nake gani,sannan yana kara ramar dani.Dan Allah malam a taimaka min da magunguna na musulunci DA zan yi amfani dasu domin samun lafiyata.
daga wata baiwar Allah.

AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Acikin magungunan Musulunci babu abinda ke magance matsalar ciwon Sugar (Diabates) fiye da Hulbah (Fenugreek). Tana kunshe da sinadarin Insulin wanda ke taimakawa wajen samar wa Jikin majinyacin abinda yake bukata.

Don haka ki nemi garin Hulba cokali 7, garin Zaitun Cokali 7, Garin Fijil Cokali 7. Garin ganyen Gwanda cokali 7. Ki gaurayasu waje guda sannan ki rika diban cokali 2 kullum kina dafawa kina sha. Bayan haka kuma kullum ki rika shan cokali 1 na Man habbatus Sauda safe da yamma.

In sha Allahu Sugar din zai rika daidaita. Kuma zaki samu kuzari ajikinki, Kuma fitsarin ma zai daidaita in Allah yaso ya yarda.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU (23-03-2016).

Comments

  1. Allah yabada lada yaqara lafiya

    ReplyDelete
  2. Allah Ya Saka Da Alkhairi, Mun Gode

    ReplyDelete
  3. Assalmu Alaikum,don Allah inason ataimaka min da nau'in abincin daya kamata ace mai ciwon suga yanaci domin rigakafi ko daidaita ta,sannan da nau'in abubuwan daya kamata mutum ya nisanta,nagode daga dan uwa a addinin musulunci.

    ReplyDelete
  4. Aslww don't Allah ganyen mangoro yana maganin suga

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI