NASIHA NASIHA NASIHA

Kowanne mutum yana yin kyauta ne da irin dukiyar gidansu.

Don haka idan Mutum ya jefo maka Baqar magana ko ya zageka, Shi irin kayan gidansu kenan. Kai kuma yi Qokari ka danne fushinka ka mayar masa da kyakkawa ko kuma kayi shuru ka kyaleshi.

Yin afuwa ga wanda ya chucheka musamman alokacin da kake da ikon ramawa ko daukar mataki akansa, Ba Qaramin abu bane.

Manzon Allah (saww) yace "Duk wanda ya danne wani fushi alhali yana da ikon zartar dashi, to aranar Alqiyamah Allah zai yi kiransa agaban dukkan halittu yace masa "SHIGA ALJANNAH DUK TA INDA KASO".

Babu wata ribar da zaka ci idan kayi jayayya ko Musu ko ramukon zagi ko cin mutunci. Amma lallai riba mai yawa tana tare dakai alokacin da kayi shuru ka danne fushinka.

Allah yasa mu gane.

DAGA ZAUREN FIQHU (02-03-2016).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI