KU DUBA WANNAN GIRMA!!

KU DUBI WANNAN GIRMA!
***************************
Sayyiduna Abu Hurairah (ra) yace "Watarana muna sallar Isha'i tare da Manzon Allah (saww). Idan yayi Sujadah sai Al-Hasan da Al-Husain (ra) suyi tsalle su hau kan bayansa.

Idan zai dago kansa, dai ya sanya hannunsa ya rikesu ta bayansa ahankali, ya saukesu daga kan bayansa.

Kuma idan ya sake (yin Sujadar) sai su komo. (Wato su sake hawa bayansa).

Har sai da ya idar sai sallarsa dai ya darasi bisa chinyarsa.

Sayyiduna Abu Hurairah yace: "Ya Rasulallahi shin in mayar dasu ne?" (wajen mahaifiyarsu?).

Nan take sai wata Walkiya ta hasko wajen. Sai Manzon Allah (saww) yace musu "KU TAFI WAJEN MAHAIFIYARKU".

Walkiyar nan bata bace ba, taci gaba da haska musu hanya. Har sai da suka shigo wajen Mahaifiyarsu (Tsira da amincin Allah gareta da Mahaifinta).

Acikin wata ruwayar kuma Abu Hurairah (ra) yace : "Al-Hasan (ra) ya kasance awajen Manzon Allah (saww) acikin wani dare mai tsananin duhu. Kuma Manzon Allah (saww) ya kasance yana Sonsa, Soyayya mai tsanani.

Sai Al-Hasan din (RA) yace: "In tafi wajen Mahaifiyata?".

Sai Abu Hurairah yace "Shin in tafi tare dashi ne, Ya Rasulallahi?".

Sai ANNABI (saww) yace "A'a".

Sai wata irin Walkiya tazo daga sama (ta haska masa hanya) yana tafiya acikin haskenta har sai da ya isa wajen Mahaifiyarsa".

ZAUREN FIQHU :
*****************
Wannan Qissar tana nuna irin Mu'ujiza ne irin na Manzon Allah (saww). Da kuma Karamah irin ta Sayyiduna Al-Hasan (ra). Sannan kuma tana nuna mana irin

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI