FADAKARWA MAI GIRMA
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Abut Tufayl (ra) ya bada labari cewa Azamanin Annabi (saww) akwai wani mutum wanda aka haifa masa yaro.
Sai ya daukoshi ya kawo wajen Manzon Allah (saww). Sai Annabi (saww) ya karbeshi ya sanya hannunsa mai albarka akan goshinsa.
Nan take sai wani irin gashi mai mutukar kyawu kamar gashin wuyan doki ya tsiro akan goshin yaron. Har yaron ya girma gashin yana nan.
To lokacin da Khawarij suka fito, sai wannan yaron yabi irin ra'ayinsu. Sai gashin nan ya zube daga goshinsa.
Mahaifin nasa da yaga haka sai ya kamashi ya kulleshi agida, ya hanashi fita don kar ya koma wajensu.
Abut Tufayl yace sai muka shiga wajensa mukayi masa wa'azi muka ce masa "Shin yanzu baka ganin albarkar Manzon Allah (saww) wacce take tare dakai gashi nan ta Zube?".
Bamu gushe ba, muna yi masa wa'azi har sai da ya tuba ya dawo daga kan ra'ayinsu. Sai Allah ya dawo masa da wannan gashin akan goshinsa tunda ya tuba.
Wannan Mu'ujiza ce mai girma daga Sayyiduna Rasulullahi (saww). Tana nan arubuce cikin littafin MU'UJIZATIR RASOOL (SAWW) NA DR. MUSTAPHA MURAAD. Shafi na 162, Mu'ujiza ta 318.
ZAUREN FIQHU
****************
Wannan hadisin yana karantar damu :
1. HALASCIN NEMAN ADDU'A DAGA WAJEN MUTANEN KIRKI.
2. Albarkar dake tare da Jikin Manzon Allah (saww) madaukaki.
3. Illolin dake tare da bin ra'ayin masu Tsatsauran/Karkatacciyar Fahimta a addini.
4. Mutukar mutum yabi ra'ayin fandararrun Mutane, to kowacce irin albarkar dake tare dashi gushewa takeyi.
5. Muhimmancin dawo da yaranmu akan tarbiyya tagari, ta kowanne hali. Koda zai kai ga mun hanasu fita wajen miyagun mutane ne.
Ya Allah ka shiryemu, ka shirya mana Zuriyya. Ka kiyayemu daga dukkan hanyoyin 'bata. Ka barmu akan tafarkin Manzonka (saww).
Ya Allah ka tsare mana imaninmu Zahiran wa Batinan. Aaameeen.
Anyi karatun a Zauren Fiqhu Whatsapp -1 ranar Alhamis 17-03-2016.
Comments
Post a Comment