ADDU'A DAGA BAWAN ALLAH MAI RAUNI ZUWA GA UBANGIJINSA MAI JIBINTAR LAMARINSA

Ya Allah Ya Ubangijin Jibreelu da Mika'ilu da Israfeel!!

Ya Ubangijin Annabi Ibraheem da Annabi Isma'eelu da Annabi Is'haqa da Annabi Musa da Annabi Eisa (as)!!
Ya Ubangijin Annabi Muhammadu (saww).. Ya Masoyin Annabi Muhammadu (saww). Ya Masoyin bayinsa masu Ikhlaasi!

Ya Mafi Jin-Qan Masu Jin-Qai, Ya Mafi Tausayin Gajiyayyu!! Ya Mai taimakon Raunana!!

Ya Mai amsa rokon masu Roko!! Ya mai bayarwa ba tare da lissafi ba! Ya mai yafewa ba tare da ba tare da Hisabi ba!!

Ya Allah muna godiya gareka bisa dukkan Ni'imomin da kayi mana afili da boye. Wadanda muka sani da wadanda bamu sani ba. Hakika Kai mai yawan kyauta ne ga bayinka.

Ya Allah ka gafarta Zunubanmu, ka shafe kusakurenmu, Ka Warkas da Zukatanmu masu Jinya, Ka 'dora karayar Jikkunanmu.

Ka shayar da Qishirwarmu, ka Qosar da yunwarmu. Ka Suturta tsaraicinmu. Ka rufa asiranmu, Ka Qarfafi rauninmu!

Ya Allaah ka albarkaci rayuwarmu, Ka shirya dukkan Zuriyarmu, Ka ilmantar damu daga Jahilci. ka raya zukatanmu da Ambatonka, ka cikamu da tsoronka. Ka Azurtamu da Bautarka, Ka kyautata Karshenmu, Kasa mu cika da kalmar SHAHADA :

LA ILAHA ILLAL LAHU MUHAMMADUR RASULULLAH (SALLAL LAAHU ALAIHI WA AALIHI WA SALLAM).

Aaaameeeen Ya Allah ka amsa don tsarkin Mulkinka da buwayarka da Qahriyyarka bisa dukkan halittunka!

Salati da aminci su tabbata bisa Shugaban Ma'aika Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa masu albarka.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (08-03-2016).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI