HANYOYIN SHIGA ALJANNAH (025)

HANYOYIN SHIGA ALJANNAH (025)

TAUHEEDI DA IKHLASI
***********************
Hadisi daga Sayyiduna Abdullahi bn Mas'ud (ra) yace:

"DUK WANDA YA MUTU BA YA YIN SHIRKA GA ALLAH, TO ZAI SHIGA ALJANNAH".

# Muslim ne ya ruwaito hadisin. aduba Tafsirin Ibnu Katheer juzu'i na 2 shafi na 189.

BAYANI
********
Tawheedi shine babban dalili ko kuma hanya, ko kuma shaida (Ticket) wanda yake lamunce ma mutum samun duk wata alfarma alahira.

Babu wanda zai samu damar yin cheto, ko kuma samun cheto awajen Allah ko Annabinsa (saww) ko Sahabbai ko Mala'iku ko Salihan bayin Allah sai wanda ya mutu da Imani.

Don haka ya kamata mu nemi ilimi mu san shin menene Imani, Kuma yaya ake Ingantashi, kuma menene yake warwareshi! Domin Wallahi Mumini bashi da wata kadara mai tsada agareshi fiye da Imaninsa.

Shi dai imani, Qudiri ne azuciya, da Furuci a baki, da kuma ayyuka na gabobi.

Imani yana Qaruwa ta hanyar yawaita ayyukan alkhairi. kuma yana raguwa ta hanyar yawaita sa'bon Allah. Kuma babu abinda ke ingantashi sai Ilimin sanin Allah da kuma yadda za'a tsaftace zuciya ta samu Ikhlasi da dawwamar Mushahada da Muraqabar Ubangijinta.

Imanin mutum yana zubewa wani lokacin ba tare da sanin mutumin ba. Musamman ta hanyar abubuwa kamar haka :

- Bidi'o'i da haramtattun abubuwa.
- Haramta halal, ko kuma Halatta haram.
- Kafirta Musulmi.
- Wulakantar da ayoyin Alqur'ani ko Hadisi ko kuma wani abu mai daraja.
- Qiyayyar Annabi (saww) ko jin haushi wani daga Iyalan gidansa ko Zuriyarsa ko Sahabba

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI