FALALAR RAKA'ATAYIL FAJRI
Raka'atayil Fajri : Sune raka'o'in nan guda biyu na nafila wadanda ake yi bayan Hudowar Alfijir, kafin sallar Asubahi.
Wannan sallar tana da inganci sosai. Domin Annabi (saww) ya bata muhimmanci. Ya kasance yana yinta aduk halin da yake ciki. Koda awajen tafiya, ko azaman gida.
Nana A'ishah (rta) ta ruwaito cewa Annabi (saww) ya kasance yana karanta Fatiha ne kadai acikinta. KUMA tana yinta ne aboye. (wato yana yin karatunta a sirrance).
Daga cikin falalarta, Sayyiduna Abdullahi bn Umar (rta) ya ruwaito cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) cewa :
"Ya Rasulallahi ina so ka nuna min wani aiki wanda Allah zai amfanar Dani saboda shi".
Sai Annabi (saww) yace masa "KA KULA DA RAKA'ATAYIL FAJRI DOMIN ACIKINTA AKWAI FIFIKO (WATO FALALA)".
(Tabaraniy ne ya ruwaitoshi).
Acikin wata ruwayar kuma Abdullahi bn Umar (ra) yace "Naji Manzon Allah (saww) yana cewa :
"KAR KU BAR YIN RAKA'O'IN NAN GUDA BIYU WADANDA AKEYI KAFIN SALLAR ASUBA. DOMIN ACIKINSU AKWAI ABABEN KWADAYI".
Domin cikar fa'idah ma, ga wani Sahihin hadisin wanda Imamu Muslim ya ruwaito daga Nana A'ishah (ra) ita kuma daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"RAKA'O'I BIYUN ALFIJIR, SUN FI DUNIYA DA ABIN CIKINTA".
Don haka 'yan uwa bai kamata mu rika barin wannan falalar tana wucemu ba.
Da yawan Matasa Wasu basu yinta. Dama basu kwanciya da wuri, shi yasa suke makara. Kuma da zarar sun tashi sai su sallaci Asubah, ita kuma su kyaleka.
To lallai rashin yin RAKA'ATAYIL FAJRI ba Qaramar Asara bace agareka ya kai Musulmi!
Wannan asarar tafi asarar Biliyoyin Nairori. Domin kuwa Annabi (saww) yace TAFI DUNIYA DA ABIN CIKINTA. Don haka idan baka yita ba, kamar kayi asarar dukiyar dake cikin duniyar nan ne. Ko kuma fiye da haka.
Na san yanzu wani zai ce "Shin zan iya yinta koda bayan Sallar Asubah ce?".
AMSA : A'a. Ana yinta ne kafin sallar Asubah. Domin bai halatta kayi sallar nafila bayan kayi ta Asubahi ba. Har sai bayan fitowar rana.
Hujjah anan ita ce Sahihin hadisin da Imamul Bukhariy da Muslim suka ruwaito daga Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"BABU SALLAH (NAFILAH) BAYAN SALLAR LA'ASAR HAR SAI RANA TA FADI. KUMA BABU SALLAH BAYAN SALLAR ASUBAH HAR SAI RANA TA BULLO".
Wani Sahabi mai suna Amru bn Abisata (ra) yace "Ya Rasulallahi bani labari mana game da sallah".
Sai yace masa "KA SALLACI ASUBAH SANNAN KA JANYE DAGA YIN SALLAH HAR SAI RANA TA FITO TAYI SAMA.....".
Imamu Ahmad da Muslim ne suka ruwaitoshi).
Mafiya yawan Jamhurin Malamai suna ganin halaccin yin ramukon sallah akowanne lokaci, koda bayan Sallar Asubah din ne. Amma banda nafila.
Saboda hadisin da Imamul Bukhariy da Muslim suka ruwaito daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"DUK WANDA YA MANTA DA WATA SALLAH (TA FARILLAH KENAN) TO YA SALLACETA IDAN YA TUNA".
Amma yin nafila bayan Sallar Asubah, mafiya yawan Sahabbai duk sun karhanta yin haka. Kamar Irin su Sayyiduna Aliyu Bn Abi Talib. Da Ibnu Mas'ud da Zaidu bn Thabit da Abu Hurairah da Ibnu Umara (Allah shi yarda dasu baki dayansu).
Sayyiduna Umar kuwa, ya kasance yakan bugi mutum idan ya ganshi yana yin nafila a irin wadannan lokutan.
Hakanan Sayyiduna Khalid bn Waleed (ra) Shima yakan bugi masu yin hakan. (Wato masu yin nafila alokutan da aka hana).
Anan zan tsaya, sai WANI lokacin kuma in sha Allahu. Da fatan Allah shi amfanemu da abinda muka karanta.
An gabatar da karatun a Zauren Fiqhu -3 (28-02-2016).
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.
Comments
Post a Comment