TAMBAYA AKAN HUKUNCIN KARBAR KUDIN BIKI
HUKUNCIN KARBAR KYAUTUKA RANAR BIKI
TAMBAYA TA 1892
********************
Assalam Alaikum Warahmatullah.
Malam Allah Yasaka da Alkhairi Ya kuma Biya da Gidan Aljanna.
Malam Ina Da Wadansu Yan Tambayoyi Da fatan Allah Zai Bada Ikon Amsawa Ameeen.
1. Malam Dan Allah Menene Hukuncin Biki A Musulunci Ina Nufi Kamar yadda Mata Suke yi. Har ma da Wasu Mazan Za kaga Idan Abun Alheri Ya samu Mutum Kamar Bikin Suna Ko Bikin Aure. To Zaka ga An Kaiwa Mutum Kudi. idan Na kaiwa Mutum 2000 Shi kuma Idan Ya tashi Zai Kawo mun 4000 To Malam Haka Ya Halatta?
2. Malam shin ya dace Mutum Yayi ma Mutum HAPPY BIRTHDAY. Kaman A Social Media Zaka ga Mutane Suna Turama Junansu Birthday Wishes.
3. Malam Menene SUJUDUSH SHUKUR? Ya Kuma Akeyinta? Kuma Wanda Daliline Yasa Akeyi?
Nagode Allah Yasaka da Alkhairi Daga Dalibinka.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Eh ya halatta idan wani abun murna ya samu 'dan uwanka, kamar aure, ko haihuwa kayi masa wani abu na kyautatawa domin tayashi murna. Wannan babu haramci acikin yin haka, mutukar dai anyi domin Allah don taimakon juna.
Shima ya halatta ya karba har ma ya bada tukwici idan yana da iko. Domin kuwa Annabi (saww) ya kasance yana karbar kyautuka daga mutane har ma yana bayar da Tukwuici. Kamar yadda Imamul Bukhariy ya ruwaito daga Nana A'ishah (rta).
Amma idan ya zamanto anyi shi ne amatsayin RANCHE ko BASHI, to bai halatta idan kazo biya ka bayar da fiye da abinda ka karba ba.
Annabi (saww) yace: "DUK WANDA YA AIKATA MUKU ALKHAIRI TO KU RAMA MASA. IDAN BAKU DA IKON (RAMAWAR) TO KUYI MASA ADDU'A HAR SAI KUNJI KAMAR KUN BIYASHI ".
(Abu Dawud ne ya ruwaitoshi).
2. HAPPY BIRTHDAY da mutane sukeyi a Social Media ba wani abu bane illa bid'ah da suka Qaga. Duk da dai masu yin hakan basu daukeshi amatsayin wani Muhimmin abu ba, to amma barinsa shine yafi.
Amma kai kanka idan lokacin haihuwarka ya zagayo ya halatta kayi wata ibadah ta musamman domin nuna ma Allah godiyarka gareshi. Misali kamar hadisin nan wanda Imamu Muslim ya ruwaito cewa an tambayi Manzon Allah (saww) game da Azumin da yakeyi duk ranar Litinin. Sai yace "WANNAN RANA CE WACCE AKA HAIFENI ACIKINTA, KUMA ACIKINTA NE AKA AIKONI".
3. SAJDATUSH SHUKR : Sujadah ce wacce mutum yakeyi nan take da zarar wani alkhairi ya sameshi ko kuma anyi masa wani albishiri mai dadi.
Ibnu Maajah da Tirmidhiy sun ruwaito daga Sayyiduna Abu Bakrata (ra) yace "Manzon Allah (saww) ya kasance duk lokacin da aka zo masa da wani labari mai sanya farin ciki, yakan Fa'di yayi Sujadah".
Hakanan Sayyiduna Abubakar lokacin da labarin Kashe Musailama ya isa gareshi, ya fadi yayi Sujadah domi. godiya ga Allah.
Ana yinta ne Sujadah guda day rak. Amma malamai sunyi sabani game da sharadin alwala ga mai yinta.
WALLAHU A'ALAM
DAGA ZAUREN FIQHU 24-03-2016).
Comments
Post a Comment