RANAR DA BABU KOKWANTO


'Dora hannunka akan Qirjinka... Zakaji yadda zuciyarka take bugawa, babu dare babu rana.. tana tafiya ne bisa wani Saiti na musamman wanda Ubangijinka yayi mata tun asali.

Nisan tafiyar wannan saitin shine Gwargwadon nisan ajalinka. Kuma Ubangijinka yana sane da yawan adadin bugawar da yayi izini agareta. Idan lokacinta ya cika, ba zata jinkirta maka ba, Ba zata Qara motsi ba.

Ranar da Mala'ikan numfashinka da Mala'ikan abincinka, da Mala'ikan abin shanka zasu zo suyi bankwana dakai, suce maka dukkan rabonka na duniyar nan ya riga ya Qare.

Ranar da Iyayenka da 'Yan uwanka da iyalanka zasu kewayeka, amma ba zasu amfana maka komai ba... Ba zasu hana abinda zai sameka ya sameka ba, kuma ba zasu sanya ajinkirta maka ba, kuma ba zasu sanya a saukaka maka ba.

Wallahi duk wannan kururuwar da sukeyi TA QARYA CE! Suna yin kuka ne don tsoron halin da zasu shiga bayan rasuwarka. Amma ba wai sunayi ne domin tausaya maka akan halin da zaka shiga ba..

Kuma WALLAHI duk cikinsu babu wanda zai yarda ya maye gurbinka, wato shi adauki nasa ran amaimakon naka.. Kuma koda matarka ba zata yarda abinneku tare ba, Ballantana 'danka ko 'Dan uwanka!!!

Duk yawan dukiyar da ka tara babu abinda zasu yarda ka tafi dashi in banda Likkafanin #2,000 (Naira dubu biyu). Kuma su zasu kaika su sanyaka acikin duhun da babu haske, Gashi babu AIR CONDITIONER, babu shimfida.

Abu daya ne kawai zai taimakeka :

Aikin da ka aikata. Sadaqar da ka yawaita, Sallolinka na tsakar dare, Azuminka na tadawwu'i, Karatunka na Alqur'ani, Soyayyarka ga Salihan bayin Allah, Sai kuma yawaitar Salatinka ga Manzon Rahama (saww).

Kowanne second guda lokaci ne na musamman agareka wanda zaka iya aikata wani abu domin Guzurin wannan doguwar tafiyar da ba'a dawowa!!

Ya Allah ka bamu kyakkyawan Qarshe, kasa mu cika da Imani. Ka Haskaka Qabarinmu, ka ni'imta mana, ka dawwamar damu acikin Soyayyar Fiyayyen bayinka (saww) da yin biyayya gareshi.

NASIHA CE DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (30-03-2016)

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI