KATATUN FIQHU ASAUKAKE
KARATUN FIQHU ASAUKAKE DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (DARASI NA GOMA SHA DAYA) BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM. Salatin Allah da amincinsa da albarkarsa su tabbata ga wanda aka aikoshi domin Rahama ga dukkan Halittu. Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan bayin Allah managarta. Idan ba'a manta ba, acikin darasi na goma mun tsaya ne akan Sunnoni da mustahabban alwala, kuma muna magana ne akan Sunnah ta goma sha bakwai. Yanzu kuma zamu dora in sha Allahu. 18. SUNNAH TA SHA TAKWAS : TSANTSAME JIKI BAYAN KAMMALA ALWALA KO WANKAN JANABA : Shi wannan mustahabbi ne awajen mafiya yawan Maluman Fiqhu. Musamman idan larura ta sanya yin hakan. Wasu ma suka ce yin hakan yana daga cikin ladubba masu kyau da kuma abubuwan kiwon lafiya. Wasu kuma daga cikin Maluman fiqhu sunce yin hakan yana daga cikin halastattun abubuwa wadanda shari'a bata hana ba, kuma bata ce ayisu ba. (Wato mutum zai iya yi ko kuma barinsu). Wasu kuma Maluman sun Qirga yin h