MAGANIN MATSALAR ZUBAR JINI
MAGANIN MATSALAR ZUBAR JINI
TAMBAYA TA 1856
*********************
Assalamu alaykum! Gaisuwa irin ta addinin musulunci tare da godia akan yanda kullum kuke kara mana sani akan addini.Allah ya kara ma malam lfy da Ilimi ya kuma saka da mafificin alkhairi. Malam,ina neman taimako yar'uwa ta k fama da zubar jini kusan 4yrs nw. Dai dai gwargwado anyi magani amma har yau abun bai tsaya ba,anje hosp daga baya mun koma Islamic medicine amma cikin hukuncin Allah har ynx. Su hulba, habbatus sauda dasu zam zam duk tayi amfani dasu malam amma ba changi. Ga ta mai riko ce da addini sosai malam,duk su azkar safe da yamma tana yin su gata mai yawan ibada azumin Thurs and mondays baya wuce ta. Don Allah malam a taimaka mana dan ko haihuwa ba tayi ba.Amma an taba fada mata a hosp cewa tana da infection. Shin malam infection na sa bleeding 4 more than 30 dys? Dan Allah malam a taimaka ko Allah yasa a dace ya tsaya.Mun gode ubangiji Allah ya kara basira amin.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah wa barakatuh.
May be su Likitocin Bincikensu ne ya nuna musu hakan, ko kuma watakil Harsashe kawai sukeyi saboda abun yafi Qarfin bincikensu. Wato su kasa gano inda matsalar takd.
To amma mu a Likitancin Musulunci, Akwai hadithi wanda Manzon Allah (saww) yake gaya ma Sayyidah Hamnatu bintu Jahshin yayain da ta samu irin wannan matsalar cewa :
"WANNAN BA KOMAI BANE FACHE ZUNGURA NE DAGA SHAITAN".
(Bukhariy da Muslim da Tirmizy da Abu Dawud da Ibnu Maajah ne suka ruwaitoshi).
Bayan haka kuma mun sha yin ruqyah akan irin wadannan Matsalolin kuma ana kama Aljanin, har ma kaji yana bayanin cewa shine yake Zungurar Mahaifarta shi yasa yake zubar mata da wannan Jinin.
Shawarar da zan baki anan ita ce Ki garzaya da 'Yar uwar nan taki wani waje Amintacce mafi kusa domin ayi mata Ruqyah, ko kuma ki kawota nan Zauren Fiqhu idan akusa damu kuke. (Amma yanzu bana Nigeria. sai bayan 22- feb za'a iya samuna).
Bayan haka ku nemi :
- HABBUR RASHAD.
- FIJIL.
- KUSTUL HINDI.
- HABBATUS SAUDA.
- GARIN FUREN ALBABUNAJ.
Kowannensu kamar cokali biyar biyar. Ki chakudasu sannan ki rika diban cokali biyu kina dafawa kullum kina bata tana sha da zuma.
In sha Allah jinin zai tsaya. Kuma zata samu lafiya. Amma dai ina recommending din lallai ki kaita ayi mata Rukyah din nan.
WALLAHU A'ALAM..
(DAGA ZAUREN FIQHU 09-02-2016)
Comments
Post a Comment