MAGANIN HANA DAUKAR CIKI
TAMBAYA TA 1857
********************
Assalamu alaikum Malam. Allah ya saka maka da alkhairi bisa wannan aiki mai albarka da kake gudanarwa.
Tambaya ce dani kamar haka: Ni Mace ce mai saurin daukar Ciki. Yanzu haka ina da yara guda bakwai. Amma dukkansu tsakaninsu ba ya Wuce Watanni Uku ko hudu nake sake samun wani Juna-biyun. Amma dai daga ni har yaran dukanmu muna cikin koshin lafia.
To shine Wata likita ta bani shawarar cewa ya kamata inyi allurar Family Planning. To ni kuma ina so, amma ina tsoron Illolin dake tare da al'amarin. Shine nake neman shawara daga gareka. Allah ya saka da alkhairi.
Masu yiwa wannan zauren Zagon-Kasa kuma, Allah ya shiryesu. Fatanmu dai Allah ya kiyayeka, ya kiyaye mana wannan zauren mai albarka. Bissalam. Dag dalibarka.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullah wa barakatuh.
Da farko dai ya kamata mu kalli Haihuwa amatsayin wata kyauta ce ta Musamman wacce Allah yake yiwa bayinsa domin ya jarrabesu.
Sannan sai mu kalli naki yanayin. Tunda ke da kanki kince wannan saurin daukar cikin bai haddasa miki wata jinya ba, Kuma kina haihuwar Jariranki cikin koshin lafiya. Ina ganin bai zama lallai sai kinyi wannan Family Planning din ba. Sai dai in rashin yin hakan zai chutar da lafiyarki.
Amma akwai wasu hanyoyin da zaku iya bi dake da maigidanki domin samar da tazarar haihuwa atsakanin 'Ya'yanku. Misali :
1. Ki rika shayar da 'ya'yanki da kanki, da ruwan nononki Zalla. Kar ki rika amfani da Madarar Kanti. Domin kuwa yayin da mace take shayar da Nono ga jaririnta, Jininta na haila ne Allah yake juyar dashi ya tsarkakeshi ya zama ruwan nonon da jaririnta zai sha.
Kuma mutukar mace bata yin haila, to sinadaran dake cikin mahaifarta basu yin shirin daukar Ciki. Wato ciki ba zai shiga ba. (Duk da dai akwai matayen da sukan dauki ciki koda suna shayarwar sosai).
2. Zaku iya daidaitawa da Maigidanki (in har ya amince) Ku rika jinkirta saduwa da juna acikin Makonni biyu na bayan daukewar hailarki. Domin acikin wannan tsakanin ne yawancin Mata suke daukar ciki.
Amma zaku iya saduwa acikin kwana biyu (wato 48 hrs) na bayan kinyi tsarkin jinin hailarki. shima awannan tsakanin, ba'a cika samun juna biyu ba.
Amma idan duk wadannan dabarun basu yi amfani gareku ba, Kuma rashin yin family planning din zai iya chutar dake ko kuma jaririnki, to shikenan sai kije kiyi. Amma ki nemi amincewar Mijinki, da kuma shawarwarin Kwararrun Likitoci.
WALLAHU A'ALAM.
ZAUREN FIQHU (10-02-2016).
Comments
Post a Comment