AFUWA DA RANGWAMEN ANNABINA (SAWW)

AFUWA DA RANGWAMEN ANNABINA (SAWW)

Ranar da yaci garin Makkah da yaki, rannan suka ga karamci da mutunci irin wanda bau taba faruwa ba, atarihin duniya..

Da chan lokacin da yake garin Makkah, manyan garin su suka fi kowa chutar dashi.. Har daga karshe sukayi yunkurin yi masa Kisaan gillah.

Amma awannan ranar da ya samu nasarar cinsu da yaki, ya kamasu gaba daya ahannunsa.. Ga manyan jarumansa nan suna jira ya basu umurni su fille wuyan kafiran nan...

Annabina (saww) yayi kirari ga Ubangijinsa, ya gode masa, sannan ya juyo wajen manyan kafiran nan yace musu:

"MAI KUKE TSAMMANI ZANYI MUKU?"

Su kuma saboda sun riga sun san kyawun halinsa da rangwamensa, sai suka ce "AFUWA ZAKAYI MANA. YA KAI 'DAN UWA MAI KARAMCI, KUMA 'DAN 'DAN UWA MAI KARAMCI!!".

Sai Annabina yace musu "To ku tafi na 'yantar daku (wato nayi muku afuwa).".

Wannan shine halin Annabina (saww). Shin acikinmu waye zai Iy kwatanta wannan halin?? Yin afuwa ga manyan makiyanka adaidai lokacin da kake da cikakkiyar dama akansu!!!.

DAGA ZAUREN FIQHU.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI