TSARKIN JIKIN MANZON ALLAH (SAWW)


Manzon Allah (saww) Mutum ne ajinsinsa, Amma ba mutum ne kamar kowa ba. Koda acikin Annabawa da Manzanni babu kamarsa, babu irinsa aduk ma'aunin da zaka gwadashi.

Shi Tsaftatacce ne wankakke. Babu dau'da ko datti ko Qazanta ko Najasa tare dashi.. Duk abinda ya fito daga jikinsa Qamshi yakeyi. Babu wari ko Qarni kamar na mutane.

Tufafinsa bai ta'ba yin Datti ba. Qura bata sauka akan fatar Jikinsa. Quda ko sauro bai ta'ba sauka kan fatar jikinsa ba (saww).

Ummu Aiman (ra) ta dauki bawalinsa amma don Qamshinsa da dadinsa bata gane cewa bawali bane. Ta dauka ta shanye. Tun daga wannan ranar ta samu waraka daga wani Ciwon ciki da take fama dashi. Kuma bata sake yin jinya ba, har ta bar duniya.

Abdullahi bn Zubair (ra) anyi ma Manzon Allah (saww) Qaho, ya bashi jinin da aka fitar, yace masa yaje ya zubar. Amma shi sai ya shanye. Albarkacin wannan jinin da ya kurba sai da ya zama babban Malami mai ilimi. Kuma babban Jarumi afagen fama. hakanan Zuriyarsa ma.

HUMAISA'UL ANSARIYYAH (UMMU SULAYM) - Allah shi yarda da ita -.Ta kasance tana tarewa guminsa (Wato Zuffa) wanda ke fitowa daga jikinsa mai daraja (saww). Idan ta zuba acikin Turarenta sai turaren ya Qara Qamshi fiye da dukkan wani turare. Tana shafa ma 'Ya'yanta don neman albarkar MA'AIKI (saww). Kuma dukkansu sunyi albarka. Sai da ta samu Mahaddatan Alqur'ani fiye da guda goma acikin 'ya'yanta da jikokinta.

YAWAN BAKINSA : Yayi tofi cikin idanun Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (ra) aranar Yaqin Khaybara. Nan take idanun suka warke, Kuma har abada basu sake yin ciwo ba.

Yayi tofi cikin idon Qataadah (ra) Yayin da idonsa ya fashe bayan an harbeshi da kibiya aranar Yakin Badar. Amma nan take idon ya warke. Har ma yafi 'dayan kyau da haske da kuma gani sosai.

Yayi tofi akan Qafar Abdullahi bn Ateek (ra) bayan ta karye ta ragargaje. Amma nan take ta koma ta hade. Babu tabon babu Miki, kuma babu ciwo.

An sare ma wani Sahabinsa kafada (Wato an tsagashi guda biyu) awajen yaqi. Ya kamashi ya jonashi sannan yayi tofi awajen. Nan take ya warke kuma yaci gaba da yaqi har sai da nasara ta samu.

Yayi tofi acikin rijiyar Hudaibiyyah wacce ta dade da Qafewa. Amma nan take ruwa ya bulbulo ta cikinta, tana ambaliya har waje. Kuma anfi shekaru 500 ana shan ruwan cikinta bai Qare ba!!

Akwai wata rijiya a Yemen. Ruwan gishiri gareta. Amma tunda watarana mutanen garin Suka je Madina wajen Manzon Allah (saww) suka Musulunta sai suka gaya masa zancen rijiyar tasu. Yace su kawo ruwa acikin guga. Yayi tofi aciki sannan yace Su tafi dashi su zuba cikin rijiyar. Tun daga wannan ranar babu rijiyar da ta kaita dadin ruwan sha.

Wata Karuwa Marar kunya tazo wucewa alhali Manzon Allah (saww) yana cin Kilishi tare da Sahabbansa (ra).  Ta rokesu nama, Sun bata amma sai tace ita irin na bakin Manzon Allah (saww) take so. Tunda ya bata taci, Nan take Imani da kunya da Mutunci suka ratsa cikin zuciyarta. Sai da ya zama ana labarin nagartar halayenta acikin Madeena.

GASHIN KANSA : Sili guda na gashin kansa yafi duniya da abin cikinta. Idan na jika silin gashinsa acikin ruwa, duk marar lafiyan da yasha ruwan nan take zai warke daga chutar da take damunsa.

Zauren Fiqhu : Da ba don kar in tsawaita ba, da sai na kawo Mu'ujizozi sama da fuda hamsin wadanda suka faru ta sanadiyyar abinda ke fitowa ta Jikinsa mai Tsarki (saww).

Fatan Zauren Fiqhu shine Allah yasa duk wanda ya karanta wannan rubutun yaji Zuciyarsa ta Qara son Annabi (saww). Da ganin fifikonsa bisa dukkan halittu baki daya.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (Wed 10th Feb 2016).

www.facebook.com/zaurenfiqhu1

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI