SIFFAR MURMUSHIN MANZON ALLAH (SAWW)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Salati da amincin Allah su tabbata bisa Jagoran Annabawa da Manzanni, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa Madaukaka.
Manzon Allah (saww) shine mafi alkhairin dukkan mutane. Shine Mafificinsu wajen daraja da Muqami da kyawun halitta da kyawun halaye.
Ya kasance ko yaushe shi Zuciyarsa tana tare da Ubangijinsa. Don haka ko yaushe cikin tunani yake akan lamarin addinin da Allah ya aikoshi dashi.
Babu abinda ke shagaltar dashi ballantana har ya rika kyalkyala dariya ko cira Muryarsa ko kuma duk wani irin yanayi kamar yadda mafiya yawan mutane sukeyi.
Shi ya zamanto Nitsatse ne, wanda yake Qawace da kyawawan dabi'u. Kuma acikin mafiya yawan lokuta yakan sunkuyar da kansa Qasa ne domin kunya.
Yana da wushirya atsakanin hakoransa masu daraja. Iab yana murmushi haske ne ke fita ta cikin wushiryar (saww).
Akwai hadisi acikin Sahihu Muslim daga Sayyiduna Jabir bn Samurah (ra) yana cewa :
"Manzon Allah (saww) ya kasance mutum ne mai yawan yin shuru. Kuma mai Qaranci dariya".
Amma fa wannan ba wai yana nufin cewa shi yana 'daure fuskarsa bane. A'a shi mai yawan fara'a ne, mai yawan sakin fuska ne ako yaushe.
Wadannan halayen guda biyu, wato :
- YAWAN YIN SHURU.
- QARANCIN DARIYA.
Halaye ne wadanda ya kamata kowanne Mumini ya zama mai koyi dasu ako yaushe.
Tabbas babu shakka halaye ne wadanda zasu taimaka ma mutum wajen ajiye duniya a muhallinta, sannan mutum ya samu mayar da hankali kan abinda aka halicceshi dominsa. Wato Ibadah da tafakkuri acikin lamarin Allah da Manzonsa (saww).
Ubangiji yana cewa : "SHIN KUNA TSAMMANIN KAWAI MUN HALICCEKU NE DOMIN WASA, KUMA KU BA ZA'A DAWO DAKU ZUWA GAREMU BA?".
(Suratul Mu'umineen ayah ta 115).
Acikin Hadisin da Imamul Bukhariy ya ruwaito, Nana A'isha (ra) tana siffanta yadda Manzon Allah (saww) yake, sai tace :
"BAN TA'BA GANIN MANZON ALLAH (SAWW) YANA DARIYA HAR IN HANGI CHAN CIKIN BAKINSA BA. SHI DAI KAWAI YAKAN YI MURMUSHI NE".
Don haka abinda Sunnar Manzon Allah (saww) ta nuna shine mu Qaranta yawan dariya Kwarai da gaske, Sanna mu yawaita sakin fuska tare da murmushi.
Yazo acikin Sahihin hadisi daga Sayyiduna Abdullahi bn Al-Harith (ra) yana cewa : "Ban ta'ba ganin wani Mutum mai yawan yin murmushi irin Manzon Allah (saww) ba".
Acikin wata ruwayar kuma cewa yayi "Dariyar Manzon Allah (saww) bata kasance ba, illa kamar murmushi".
Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (ra) yace "Manzon Allah (saww) bai ta'ba buya gareni ba, tunda na Musulunta. Kuma Annabi (saww) bai ta'ba ganina ba, har sai yayi mun Murmushi". Domin shi yin murmushi da zarar kun hadu da dan uwanka Musulmi, shima sadaqah ne.
Hakika Manzon Allah (saww) shine mafi Fasahar harshe acikin mutane. Kuma shine mafi dadin zance. Kuma mafi Zaqin murya wajen magana. Kuma shine wanda zancensa yadi na kowa saurin shiga zukatan mutane.
Murmushinsa ya kasance yana kunshe da dukkan Ma'anoni mafiya kyawu. Da kuma manufofi mafiya girma. Don haka murmushin nasa ya zamo daga cikin Siffofinsa mafiya kyawu, da kuma dabi'unsa mafiya tsarki.
Wani lokacin murmushin nasa yakan zamanto hanya ce ta tarbiyyar al'ummah, ko fuskantar dasu, ko kuma don jawosu ajiki, ko kuma don saukakawa garesu.
Annabi (saww) bai ta'ba yin zance ba tare da ya hada da murmushi ba. Don haka ya zama mafi kyauwun zuciya acikin mutane.
Ya kasance wani lokacin yakan yi murmushin sosai yadda har dasashin hakoransa yakan fito. Amma ba tare da ya hada da 'daga sauti ba.
Kharijatu bn Zaid (ra) yace "Manzon Allah (saww) ya kasance mafi girmama mutane awajen zamansa. Domin babu wani abinda yake kubce masa. Yana kallon komai, amma ba ya magana sai da bukatar hakan.
Yakan kau da kansa ga duk wanda yayi zance marar dadi. Kuma dariyarsa ta zamanto Murmushi ce.
Zancensa kuma dalla-dalla yake yinsa. Ba ya tsawaitawa, kuma ba ya Gajartawa fiye da kima. Hakanan su ma Sahabbansa idan suna tare dashi basu yin irin dariyar nan wacce mutane suke kyalkyalawa. Sai dai suyi murmushi saboda nutsuwarsu, koyinsu dashi, Da kuma girmamawa gareshi.
Sayyiduna Abu Hurairah (ra) yace "Manzon Allah (saww) ya kasance idan yana murmushi sai kaga haske kamar Walkiya ajikin bango (wato garu).
(ABDURRAZAQ ne ya ruwaito acikin ALMUSANNAF).
Yana daga cikin koyarwar Manzon Allah (saww) cewa mutum ya Qaranta dariya, kuma ya dena kaiwa maqura wajen dariyar da zai yi. Domin kuwa ya gaya ma Sayyiduna Abu Hurairah (ra) cewa :
"YA ABA HURAIRAH! KA QARANTA YIN DARIYA. DOMIN YAWAITAR DARIYA YANA KASHE ZUCIYA".
(Ibnu Maajah ne ya ruwaito).
Ibnul Qayyim ya fada acikin Zadul Ma'ad yana cewa "Manzon Allah (saww) ya kasance yakan yi dariya daga abinda suke yin dariya akansa (wato sahabbansa kenan) Musamman akan abubuwan Mamaki, ko kuma baqin abubuwa. Sai dai mafi yawan dariyarsa, murmushi ce.
Musamman wani lokacin idan sun tuno zantukan yarinta, ko kuma abubuwan da suka faru alokacin jahiliyyah. Idan sunyi dariya shi kuma yakan yi murmushinsa (saww).
Kamar yadda yazo acikin Sahihu Muslim, Sammaak bn Harbin yace "Na tambayi Jabir bn Samurah (ra) "Shin ka kasance kana zma tare da Manzon Allah (saww)??
Sai yace "Kwarai kuwa. Sau da yawa ma. Ya kasance ba ya tashi daga wajen da ya sallaci Asubah har sai rana ta fito. To idan rana ta fito yakan tashi.
Su kuma alokacin nan Sahabbai suna waje suna hira. Sukan tuno da al'amura irin na lokacin jahiliyyah. Sukan yi dariya, shi kuma yakan yi murmushi".
Wani lokacin kuma acikin Sahabbansa akan samu wasu mutane wadanda su dabi'arsu ne suna da yawan yin abubuwan barkwanci wadanda zasu sa ayi dariya.
Kamar yadda Imamul Bukhariy ya ruwaito daga Sayyiduna Umar bn Khattab (ra) yana cewa "Azamanin Manzon Allah (saww) akwai wani Mutum mai suna Abdullahi, amma ana yi masa lakabi da "Himaar". Ya kasance yana ba ma Manzon Allah (saww) dariya".
Daliban Zauren Fiqhu daga cikin wannan karatun na yau zamu iya cirar fa'idodi masu yawa. Daga ciki akwai :
- Rashin kyaun Kyalkyala dariya.
- Mujimmancin yin murmushi.
- Taushin hali irin na Manzon Allah (saww).
- Kusancinsa da Sahabbansa.
- Illolin Kyalkyala dariya.
Etc.
Allah ahi taimakemu. Allah shi Qara mana Son Manzon Allah (saww) da koyi dashi acikin dukkan lamarinmu. Aaameeen
An fara karatun a ZAUREN FIQHU WHATSAPP 2, Kuma an Qarasa a ZAUREN FIQHU WHATSAPP 4 yau asabar 13 - 02-2016.
Jakallahu khair
ReplyDelete08032540154
Abdullahi
Don Allah A taimaka a sani a whatsapp