Posts

Showing posts from July, 2015

HIKIMOMI DAGA TASKAR MA'AIKI SAWW (1)

Kalmomi ne jerarru cike da hikimomi da wa'azozi, kumq sun fito daga bakin wanda ba ya fada son rai. Ba ya magana sai da wahayi daga Rabbul Izzati. Ga kadan daga ciki: 1. Manzon Allah (saww) yace: "MUTUM HUDU, HAKKI NE AKAN ALLAH CEWA BA ZAI SHIGAR DASU ALJANNAH BA, KUMA BA ZAI DANDANA MUSU NI'IMOMINTA BA : - MAI KWANKWADAR GIYA. - MAI CIN RIBAA (KUDIN RUWA - INTEREST). - MAI CIN DUKIYAR MARAYA BA TARE DA HAKKI BA. - MAI BIJIRE MA IYAYENSA. (Imamul Hakim ne ya ruwaito hadisin acikin Mustadrak). Wannan hadisin gargadi ne zuwa ga dukkan Musulmi. Idan an ce MAI KWANKWADAR GIYA, ana nufin har masu shan kwaya, da masu shan Weewi, da sauran kayan maye. Domin duk abinda ke bugarwa shima giya ne. MAI CIN RIBAA - Wannan gargadi ne ga masu hulda da bankuna, da masu hulda da kampanonin Inshaura (Insurance companies) da masu huldar kasuwanci da Ma'aikatan Gwamnati. Sai a kiyaye domin shi Allah ba ya mantuwa. kuma yana nan a madatsa zaka je ka iskeshi, Kuma zaka karbi sakam

SHIN KA TABA ZUBDA HAWAYE SABODA TSORON ALLAH??

Zubar da hawaye saboda tsantsar tsoron Allah yana daga cikin halayen bayin ALLAH na kwarai. Musamman Annabawa, Sahabbai, da waliyyan Allah. Acikin Mutanen da zasu shiga Inuwar al'arshi aranar da babu wata inuwa sai ita, Manzon Allah (saww) ya Qirga har da mutumin da ya tuna Allah shi kadai aboye, har idanunsa suka zubda hawaye. Annabi Dawud (as) ya kasance mutum ne mai yawan zikirin Allah. Har ma Ubangiji ya hore masa duwatsu da Tsuntsaye suna yin Tasbeehi tare dashi. Manzon Allah (saww) yace: "MUTANE SUN KASANCE SUNA ZUWA SUNA GAISAR DA ANNABI DAWUD, SUNA ZATON KAMAR BASHI DA LAFIYA NE.. AMMA BABU KOMAI GARESHI IN BANDA TSORON ALLAH". Wato wannan ya faru ne saboda ramewa da kuma bayyanar alamomin jinya agareshi. amma ba jinya bace.. Tsoron Allah ne yayi ka-ka-gida azuciyarsa. Hamran bn A'ayun ya ruwaito cewa Manzon Allah (saww) ya karanta ayoyin nan na cikin Suratul Muzammil wato "إن لدينا أنكالا وجحيما  وطعاما ذا غصة وعذابا

GA SADAQAH JARIYAH GARWMU BAKI DAYA

Ga wata fa'idah nan daga ZAUREN FIQHU zan bada ita amatsayin SADAQATUN JARIYATUN. Addu'a ce daga Manzon Allah (saww) wacce anfaninta ba zai Qirgu ba. Duk wanda yake son Allah ya kiyayeshi daga sharrin Munafurci, ko kallon haramun, ko Zina, ko dangogin zinar, ko Sata, ko kuma duk wani mummunan hali, idan yana yin wannan addu'ar tare da ikhlasi In sha Allahu  Ubangiji zai kiyayeshu ba zai aikata ba.. Hakanan duk wanda shaitan ya rinjayeshi yana aikata haka, to idan yana yin wannan addu'ar tare da Ikhlasi Allah zai yaye masa, zai shiryar dashi hanya Madaidaiciya. Gata nan zan rubuto da larabci, sannan in rubuto da boko, sannan in rubuto fassararta in sha Allah. اللهم إني أعوذ بك من شر سمعي, ومن شر بصري, ومن شر لساني, ومن شر قلبي, ومن شر منيي. "Allahumma innee a'uzu bika min sharri Sam'ee,  Wa min sharri Basaree, Wa min sharri Lisaanee, Wa min sharri Qalbee, Wa min sharri Maniyyee" "YA ALLAH INA NEMAN TSARINKA DA

ALBARKACIN MANZON ALLAH (SAWW

Annabi (saww) yana da albarka. Hasali ma shine yafi kowa albarka acikin dukkan halittun Allah. Duk na ani mai albarka daga wajensa ya samu. Abu Juhaifa (ra) yace: "Watarana Manzon Allah (saww) yazo wajenmu da rana sai aka kawo masa ruwa yayi Alwala. Bayan ya idar da alwalar sai Sahabbansa (ra) suka dauki sauran ragowar ruwan suna Shafawa ajikinsu. (Domin neman albarkarsa). Sai Manzon Allah (saww) ya mike yayi sallah raka'a biyu, sandansa yana kusa dashi (amatsayin Sutrah). Bayan ya idar sai yasa aka kawo masa ruwa awani Kofi, ya wanke fuskarsa da hannayensa aciki, sannan ya kurkure bakinsa ya zuba acikin Kofin. Sai ya kira Abu Musal Ash'ary da Kuma Bilal, ya basu wannan ruwan yace musu: "KU ZUBA WANNAN RUWAN AKAN FUSKARKU DA KUMA QIRJINKU" Aduba: * Sahihu Muslim juzu'I na 1 shafi na 360, hadisi na 503. * Sunanul Kubra na Imamun Nisa'iy juzu'I na 1 shafi na 126 hadisi na 135. Musnad na Ahmad bn

QISSAR YAQIN BADAR KASHI NA TARA

AN FARA GWABZAWA TSAKANIN JARUMAI Acikin kashi na takwas mun tsaya ne adaidai wajen da Kowanne bangare sukayi sahu sahu, kuma Manzon Allah (saww) yayi addu'a yana cewa: "Ya Allah Ga Quraishawa nan sun tunkaro da Alfaharinsu, suna jayayya da kai, kuma suna Qaryata Manzonka.. Ya Allah taimakon nan naka wanda kayi min alkawari". Adaidai wannan lokacin sai wani sabani ya faru atsakanin manyan Askarawan Mushrikan Makkah. Yayin da shi Utbatu bn Rabee'ah yake kokarin hana yin Yakin, yake kokarin kawai zai dauki fansa bisa dan uwan alkawarinsa wato Amru bn Alhadhramiy wanda Muminai suka kashe bisa kuskure, alokacin da suka fita wani Samame karkarin Sayyiduna Abdullahi bn Jahash. Har ya fara jan ra'ayin sauran mutanensu akan haka, da Abu Jahal ya samu labari sai yace masa "Kai dai Rago ne. Amma mu kan wallahi ba zamu koma gida ba, har sai Allah yayi hukunci tsakaninmu da Muhammadu". Ana cikin haka, Ashe su mushrikai Qishirwa ta fara cin addabarsu. Sai wani

QARFIN RUNDUNAR MUSULMAI

Duk gaba dayan wadanda suka fito tare da Manzon Allah (saww) mutum dari uku ne da sha uku (313). Ance lokacin D Manzon Allah (saww) ya Qirgasu yaga adadinsu yayi farinciki. harma ya gaya musu cewa wannan adadin shine adadin yawan Mutanen da Suke cikin rundunar 'DALUTU wadanda suka tsallake Qoram tare dashi. (wadanda Allah ya bada labarinsu acikin Suratul Baqarah). Sun tahi tare da Rakumma guda SABA'IN, dawakai kuma guda biyu Rak!!. Doki daya na Miqdadu bn Amru ne. Dayan kuma na Marthad bn Abi Marthad Alganawiy (ra). Babbar tutar yakin tana hannun MUS'ABU BN UMAIR. Amma akwai wasu Qananan tutocin Bakake guda biyu agaban Manzon Allah (saww). Daya tana hannun Aliyu bn Abi Talib (ra), dayar kuma tana hannun wani daga cikin mutanen Madinah. Daga chan Qarshen bayan rundunar kuma, akwai wani Sadaukin Sahabi mai suna Qaysu bn Sa'asa'ah Al-Ansariy (ra). Idan an dubi yadda rundunonin guda biyu suke, za'a ga cewa rundunar kafiran ta ninka yawan rundunar musulman har sa

QARFIN RUNDUNAR KAFIRAI

Adadin dakarun Mushrikan Makkah wadanda suka fito yakin badar, Su dubu daya ne (1,000). Acikinsu akwai mutum dari shida (600) suna tafiya a Qasa, suna sanye da Sulke da kwakwali da sauran kayan yaki. Sannan akwai mutum dari akan dawakai, su ma suna sanye da cikakken shirin kayan yaki. Kuma akwai Rakumma guda dari bakwai (700) tare dasu akwai  Zabiyoyi (irin fitsararrun matan nan masu rera musu wakkoki na habaici ga Musulmai). Kwamandan dake rike da tutar kafirai awannan ranar shine ASSA'IBU BN YAZEED (sannan bai Musulunta ba). ya musulunta daga baya, kuma shine Kakan na biyar ga Imamush Shafi'iy (rah). Mutum goma sha biyu ne suka dauki nauyin ciyar da Sojojin rundunar. sune kamar haka: 1. Abu Jahal (L. A). 2. Utbatu bn Rabee'ah. (L. A). 3. Shaibatu bn Rabee'ah (L. A) 4. hakeem bn Hizaam. 5. Al-Abbas bn Abdil Muttalib. 6. Abul Bakhtariy. 7. Zam'atu bn Aswad. 8. Ubayyu bn Khalaf (L. A). 9. Umayyatu bn Khalaf (L. A). 10. An-Nadhru bn Alharith. 11. Nabeeh

KAFIRAI SUN SAMU LABARIN FITOWARSA

Yayin da Shugaban ayarin kasuwancin nan na mutanen Makkah wato Abu Sufyan ya samu labari cewa Manzon Allah (saww) ya fito tare da Sahabbansa domin su taresu akan hanya, Sai hankalinsa ya tashi sosai. Don haka ya dauki hayar wani 'dan Kundumbala wanda zai nuna musu wata hanyar da zasu zage domin su kauce ma haduwa da Manzon Allah (saww). Kafin nan kuma ya dauki hayar wani mutum mai suna Dhamdhamu bn Amru Alghifariy ya turashi zuwa garin Makkah cewa yaje ya sanar da Quraishawa cewa ga ANNABI MUHAMMADU nan (saww) ya fito domin ya tare musu ayarin kasuwancinsu. Da yaje Makkah, ya hau kan wani dutse daga cikin duwatsun garin sannan ya yayyaga tufafinsa, ya rika kwarara eehu yana kiran sunayen manyan kafiran makkah yana vasu labarin halin da ake ciki. Don haka gaba dayan kafiran nan na Makkah sai tsohuwar Qiyayyar da suke ma Annabi (saww) da sahabbansa ta motsa musu. Suka tashi suka daura shirin yaki suka fito. Dukkan Manyan garin Makkah babu wanda bai fito wannan yakin ba, in banda

DALILAN YAQIN BADAR

Dalilan da suka janyo aka fito domin gwabza yakin sune kamar haka : 1. Kisan da rundunar Musulmai sukayi ma wani Mutumin Makkah mai suna Amru Alhadhramiy. 2. DAWOWAR ABU SUFYAN DAGA FATAUCI BIRNIN SHAAM. 3. KARYA QARFIN DUKIYAR ABOKAN GABA. Yadda abun yake, bayan Musulmai sunyi hijira daga Makkah Zuwa Madeenah sun bar dukiyoyinsu da gidajensu duk agarin Makkah. Sai su kafiran garin suka rika wawashe dukiyar. Suna mallakewa. To ire iren wadannan dukiyoyin ne suka hada suka bama Abu Sufyan ya tafi domin gudanar musu da fatauci. Don hakane da Manzon Allah (saww) ya samu labarin cewa Abu Sufyan yana hanyar dawowa daga Shaam, kuma hanyar wucewarsa ta kusa da garin Madeenah ne. Don haka sai Manzo (saww) yace ma Sahabbansa : "GA AYARIN QURAISHAWA NAN. ACIKINTA AKWAI DUKIYOYINSU, DON HAKA KU FITO KO ALLAH ZAI KWATO MUKU ITA". Wasu daga cikin Sahabbai suka tashi suka fito tare dashi. Wasu kuma suka zauna basu fita ba. basuyi tsammanin cewa yaki za'ayi ba. Tunda sunji lokac

YAU CE RANAR YAKIN BADAR

Wannan rana ta 18 ga Ramadhan tana daga cikin ranakun tarihi wadanda bai kamata duk wani musulmi ya manta dasu ba. Kamar shekaru 1434 da suka gabata, awannan ranar kafiran Makkah suka fito da manyan Jarumansu da Manyan Masu Hannu da shuninsu.. Gaba dayansu su 1000 (dubu daya). Duk sun fito da kayan yakinsu sun taho domin su Murkushe Musulmai da Musulunci. Shi kuma ANNABI (saww) ya fito tare da Sahabbansa 'yan kadan, su 313 ne. Kuma babu wani cikakken shirin Yaki ko manyan Makamai sosai tare dasu.. Daga Bangaren Dakarun Kafirai akwai manyan kwamandodi irin su: - A bu Jahal bn Hisham . - Shaibatu Bn Rabee'ah . - Utbatu Bn Rabee'ah . - Umayyatu bn Khalaf . Daga Bangaren rundunar Musulmai kuma , babban kwamandansu shine SAYYIDUNA MUHAMMADUR RASULULLAHI (SAWW). Amma a karkashinsa akwai Manyan Kwamandodi kamar su: - Zakin Allah da Manzonsa ( Hamzatu bn Abdil Muttalib ). - Aliyyu Bn Abi Talib ( ra ). - Zubair bn Al- awwam (ra). -  Umar bn A

GWARZON MUSULUNCI SALMANUL FARISIY (RA)

Sayyiduna Salmanul Farisy shine Sahabin da yafi dukkan Sahabbai yawan shekaru aduniya. Domin kuwa yafi shekara 100 yana jiran Zuwan Manzon Allah (saww). Wasu daga cikin Malaman tarihi sunce Shekara 170 ya ayu aduniya. Amma wasu kuma Sunce ya haura shekaru 300 ma yana raye. Watakil wadanda suka ce ya haura shekara 300 din zancensu yana da Qarfi domin kuwa Salmanul Farisy ya zauna awajen Manyan Malaman addinin Kirista masu yawa. Lokacin da ya gudo daga garinsu ya taho garin Shaam (Syria) sai ya tambayi mutanen garin cewa su nuna masa Babban Malamin addinin Nasaara (Kiristanci) Saboda alokacin nan musulunci bai bayyana ba. Sai suka nuna masa babban Paada (Bishop) na garin. Yaje ya zauna tare dashi tsawon shekaru, har mutumin nan ya tsufa basu rabu ba. har zuwa lokacin da Paadan nan ya rasu. Bayan ya rasu, Sai aka nada magajinsa. Sai Salmanul Farisy ya zauna tare da wannan magajin nasa tsawon shekaru har shima yazo rasuwa. Da yazo rasuwa sai Sayyiduna Salmanu ya tambayeshi shin Yanzu

SIFFOFIN ALJANNAH, DAGA ZAUREN FIQHU

An gina Aljannah ne da tubali (blocks) na Zinare da Azurfa tatacciya. Simintin cikinta anyishi ne da Almiski mai mutukar Qamshi. An cike tsakanin tubalanta da kayan ado na Zubarjadi da Yaaqootu. An halicci Qasar cikinta ne daga Za'afaran. Tana da Qofofi guda takwas kamar haka: 1. Jannatul Ma'awa. 2. Daarul Maqaam. 3. Daarus Salaam. 4. Daarul Khuld. 5. Jannatul 'Adni. 6. Jannatun Na'eem. 7. Jannatul Khaseef. 8. Jannatul Firdaus. JANNATUL MA'AWA ita ce daga Qasa, JANNATUL ADNI kuma ita ce matsakaiciya, JANNATUL FIRDAUSI kuma ita ce Qololuwa. Acikin Aljannah akwai Gonaki da lambuna wanda tsawon kowacce gona da fadinta ya kai tsawon tafiyar shekara 100 ko fiye da haka. Akwai bishiyoyi masu inuwa masu ni'ima da tsirrai marassa Qaya. An Halicci bishiyoyim cikinta ne daga madaukakin Zinare da tatacciyar Azurfa. Suna da manyan ganye kamar girman kunnen giwa, kuma 'ya'yan itacen bassu Qarewa. Suna nan nau'i-nau'i. Wadanda suke Qaunar juna

SIFFOFIN ALJANNAH, DAGA ZAUREN FIQHU

An gina Aljannah ne da tubali (blocks) na Zinare da Azurfa tatacciya. Simintin cikinta anyishi ne da Almiski mai mutukar Qamshi. An cike tsakanin tubalanta da kayan ado na Zubarjadi da Yaaqootu. An halicci Qasar cikinta ne daga Za'afaran. Tana da Qofofi guda takwas kamar haka: 1. Jannatul Ma'awa. 2. Daarul Maqaam. 3. Daarus Salaam. 4. Daarul Khuld. 5. Jannatul 'Adni. 6. Jannatun Na'eem. 7. Jannatul Khaseef. 8. Jannatul Firdaus. JANNATUL MA'AWA ita ce daga Qasa, JANNATUL ADNI kuma ita ce matsakaiciya, JANNATUL FIRDAUSI kuma ita ce Qololuwa. Acikin Aljannah akwai Gonaki da lambuna wanda tsawon kowacce gona da fadinta ya kai tsawon tafiyar shekara 100 ko fiye da haka. Akwai bishiyoyi masu inuwa masu ni'ima da tsirrai marassa Qaya. An Halicci bishiyoyim cikinta ne daga madaukakin Zinare da tatacciyar Azurfa. Suna da manyan ganye kamar girman kunnen giwa, kuma 'ya'yan itacen bassu Qarewa. Suna nan nau'i-nau'i. Wadanda suke Qaunar juna

FALALAR YIN ADDU'A DA KUMA MUHIMMANCINTA

BISMI LLAHIR RAHMANIR RAHEEM SALATI da amincin Allah su tabbata ga zababben Allah, shugabanmu ANNABI MUHAMMADU , ta re da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansu yardaddu . In sha Allahu zamu dora gada wajen da muka tsaya ne acikin maganar FALALAR YIN ADDU'A DA KUMA MUHIMMANCINTA. Manzon Allah (saww) yace : "HAKIKA ALLAH MADAUKAKIN SARKI RAYAYYE NE, KUMA MAI KARAMCI NE. YANA JIN KUNYAR MUTUM YA CIRA HANNYENSA GARESHI, KUMA ACE YA DAWO DASU TA'BABBU BABU KOMAI AKANSU". (Sahihul Jaami'i). Kun ga wannan hadisin yana karantar damu cewa mu rika kyautata tsamaninnu ga Ubangijinmu. Lallai shi yana jin kunyar mu rokeshi bai amsa mana ba. Awani hadisin kuma Manzon Rahama (saww) yace: "IDAN DAYANKU ZAI YI ADDU'A, KAR YACE "ALLAH GAFARTA MIN IDAN KASO". LALLAI NE MUTUM YA SANYA MUHIMMANCI CIKIN ROKONSA, KUMA YA GIRMAMA KWADAYINSA, DOMIN SHI ALLAH BABU ABINDA YAFI GIRMAN BMYA BAYAR DASHI". (Sahihul Jaami'i). Shi kuma wannan ha

YAWUN BAKIN MA'AIKINA (SAWW)

Image
Tsira da aminci su tabbata bisa Annabin da yayi tofi cikin idanun Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib. tun daga wannan ranar idonsa bai sake yin ciwo ba, kuma bai sake yin kwantsa ba. 2. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabin nan da yayi tofi sau daya acikin rijiyar Hudaibiyyah, sai ga rijiyar ta ciko da ruwa tana ambaliya. ba ta sake Qafewa ba har abada. 3. Salati irin naka na Girma ya Allah su tabbata bisa Annabin da yayi tofi cikin idanun Qatadatu, bayan idon ya fado.. ya koma ya hade. harma yafi 'dayan kyau da kaifin gani. 4. Mafi cikar amincinka Ya Allah shi tabbata bisa Annabin da yayi tofi acikin wani ruwa acikin guga, da aka mayar aka zuba cikin rijiyar gishiri ta mutanen Yemen, Ruwan rijiyar ya koma ruwan Zaqi, kuma bai taba Qarewa ba. har yau din nan yana nan. 5. Salati irin na Allah tare da daraja da daukakar martabobi su tabbata bisa Annabin da yayi tofi cikin Qaramar tukunyar abinci, amma sai da Mutane fiye da dubu uku suka ci abincin tukunyar bai Qare b