YAWUN BAKIN MA'AIKINA (SAWW)

Tsira da aminci su tabbata bisa Annabin da yayi tofi cikin idanun Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib. tun daga wannan ranar idonsa bai sake yin ciwo ba, kuma bai sake yin kwantsa ba.

2. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabin nan da yayi tofi sau daya acikin rijiyar Hudaibiyyah, sai ga rijiyar ta ciko da ruwa tana ambaliya. ba ta sake Qafewa ba har abada.

3. Salati irin naka na Girma ya Allah su tabbata bisa Annabin da yayi tofi cikin idanun Qatadatu, bayan idon ya fado.. ya koma ya hade. harma yafi 'dayan kyau da kaifin gani.

4. Mafi cikar amincinka Ya Allah shi tabbata bisa Annabin da yayi tofi acikin wani ruwa acikin guga, da aka mayar aka zuba cikin rijiyar gishiri ta mutanen Yemen, Ruwan rijiyar ya koma ruwan Zaqi, kuma bai taba Qarewa ba. har yau din nan yana nan.

5. Salati irin na Allah tare da daraja da daukakar martabobi su tabbata bisa Annabin da yayi tofi cikin Qaramar tukunyar abinci, amma sai da Mutane fiye da dubu uku suka ci abincin tukunyar bai Qare ba.

6. Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da yayi tofi cikin 'yar Qaramar jakar dabino, sai da akayi sama da shekaru Ashirin ana cin dabinon nan amma bai Qare ba.

7. Tsira da amincin Allah su tabbata bisa Annabin da Yawun bakinsa yake warkar da raunuka, ya mikar da guragu, ya shiryar da kafirai, Ya warkar da majinyata..

Hada da iyalan gidansa masu alfarma, da Sahabbansa Madaukaka.

Albarkacin wannan salatin ka sadamu da Manzon Allah (saww) aduniyarmu da lahirarmu mu kasance ko yaushe tare dashi, cikin kaunarsa, da biyayyarsa, da girmamashi.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI