DALILAN YAQIN BADAR


Dalilan da suka janyo aka fito domin gwabza yakin sune kamar haka :

1. Kisan da rundunar Musulmai sukayi ma wani Mutumin Makkah mai suna Amru Alhadhramiy.

2. DAWOWAR ABU SUFYAN DAGA FATAUCI BIRNIN SHAAM.

3. KARYA QARFIN DUKIYAR ABOKAN GABA.

Yadda abun yake, bayan Musulmai sunyi hijira daga Makkah Zuwa Madeenah sun bar dukiyoyinsu da gidajensu duk agarin Makkah. Sai su kafiran garin suka rika wawashe dukiyar. Suna mallakewa.

To ire iren wadannan dukiyoyin ne suka hada suka bama Abu Sufyan ya tafi domin gudanar musu da fatauci. Don hakane da Manzon Allah (saww) ya samu labarin cewa Abu Sufyan yana hanyar dawowa daga Shaam, kuma hanyar wucewarsa ta kusa da garin Madeenah ne. Don haka sai Manzo (saww) yace ma Sahabbansa :

"GA AYARIN QURAISHAWA NAN. ACIKINTA AKWAI DUKIYOYINSU, DON HAKA KU FITO KO ALLAH ZAI KWATO MUKU ITA".

Wasu daga cikin Sahabbai suka tashi suka fito tare dashi. Wasu kuma suka zauna basu fita ba. basuyi tsammanin cewa yaki za'ayi ba. Tunda sunji lokacin da Manzon Allah (saww) yake cewa : "DUK WANDA ABIN HAWANSA YAKE KUSA, TO YA FITO YA HAU YA TAFI TARE DAMU".

JINJIN GAREKA YA MA'AIKIN ALLAH..

Ya Allah yi salati gareshi gwargwadon fitowar rana da faduwarta, sau adadin dukkan abinda take haskawa, da kuma dukkan abinda yake amfanuwa da haskenta".

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI