SIFFOFIN ALJANNAH, DAGA ZAUREN FIQHU

An gina Aljannah ne da tubali (blocks) na Zinare da Azurfa tatacciya. Simintin cikinta anyishi ne da Almiski mai mutukar Qamshi.

An cike tsakanin tubalanta da kayan ado na Zubarjadi da Yaaqootu. An halicci Qasar cikinta ne daga Za'afaran.

Tana da Qofofi guda takwas kamar haka:

1. Jannatul Ma'awa.
2. Daarul Maqaam.
3. Daarus Salaam.
4. Daarul Khuld.
5. Jannatul 'Adni.
6. Jannatun Na'eem.
7. Jannatul Khaseef.
8. Jannatul Firdaus.

JANNATUL MA'AWA ita ce daga Qasa, JANNATUL ADNI kuma ita ce matsakaiciya, JANNATUL FIRDAUSI kuma ita ce Qololuwa.

Acikin Aljannah akwai Gonaki da lambuna wanda tsawon kowacce gona da fadinta ya kai tsawon tafiyar shekara 100 ko fiye da haka.

Akwai bishiyoyi masu inuwa masu ni'ima da tsirrai marassa Qaya.

An Halicci bishiyoyim cikinta ne daga madaukakin Zinare da tatacciyar Azurfa.

Suna da manyan ganye kamar girman kunnen giwa, kuma 'ya'yan itacen bassu Qarewa. Suna nan nau'i-nau'i.

Wadanda suke Qaunar juna domin Allah zasu samu shiga Aljannah kuma acikinta za'a basu wasu Al'amudai na Yaqootu.

Akan Al'amudan akwai Dakuna (rooms) guda dubu saba'in (70,000) masu haske.

Kuma hasken Wadannan dakunan ne zai haske 'Yan Aljannah kamar yadda hasken rana yake haske mutanen duniya.

Akwai dakunan cin abinci yalwatattu ta yadda acikin dakin cin abinci guda za'a samu shimfidu (dining sheet) guda dubu saba'in (70,00).

Akwai Qananan yara masu hidima, suna zagayawa ko ina cikin gidan Aljannah. Sunci ado da kaya iri-iri. Kuma Su kansu suna haske kamar Lu'u.

Bishiyoyin dabinai da inabi wadanda 'ya'yansu ko yaushe nunannu suke. Kuma suna daf da Qasa. Girman kowanne nonon dabono yakai kamar Zira'i 12. Kuma kowanne kwayan dabino guda ya kai girman Tulu, Kuma fari ne tas kamar madara, Kuma babu Kwallo acikinsa. Zakinsa kuma wane Zuma!!

Kuma girman kowanne Inabi guda daya yakai girman tulu.

Sai wani Sahabi yace "Ya Rasulallahi guda daya zai isheni dani da iyalaina?"

Sai Manzon (saww) yace masa "AI GUDA DAYA ZAI ISHEKA DAKAI DA KABILARKA MA BAKI DAYA".

TUFAFIN 'YAN ALJANNAH:

Kowanne Dan Aljannah za'a sanya masa riguna guda 70 na haske. Masu taushi, masu kyalli, Kuma marassa nauyi ko kadan.

Wadannan rigunan kowacce kalarta daban, nau'inta daban. Kuma ba irin tufafin duniya bane, domin kuwa babu wacce take rufe 'yar uwarta.

Saboda tsananin haskensu da kyawunsu, ana iya ganin Siffar jikin mutum har Zuciyarsa da irin Qarfin soyayyar da take dauke dashi.

Wadannan Tufafin bassu tsufa ko datti, kuma bassu yagewa.

QORAMUN ALJANNAH

Acikin Aljannah akwai Qoramu (Kogi) guda bakwai:

1. Kogin ruwa.
2. Kogin Madara.
3. Kogin ruwan Zuma .
4. Kogin ruwan giya (Sharabun Tahoorun).
5. Kogin Kafoor.
6. Kogin Zanjabeel.
7. Kogin Tasneem.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.

Ya Allah muna tawassuli da fiyayyen bayinka (saww) domin alfarmarsa ka gafarta mana kasa muna cikin 'Yan Sahun gaba wajen shiga Aljannah.

Wannan tsohon rubutunmu ne tun na bara (last year).

'Yqn uwa ga Ramadhan nan ya kusanto. Sai mu dage mu nemi Aljannah da Yardar Allah.

www.facebook.com/zaurenfiqhu1

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI