KAFIRAI SUN SAMU LABARIN FITOWARSA


Yayin da Shugaban ayarin kasuwancin nan na mutanen Makkah wato Abu Sufyan ya samu labari cewa Manzon Allah (saww) ya fito tare da Sahabbansa domin su taresu akan hanya, Sai hankalinsa ya tashi sosai. Don haka ya dauki hayar wani 'dan Kundumbala wanda zai nuna musu wata hanyar da zasu zage domin su kauce ma haduwa da Manzon Allah (saww).

Kafin nan kuma ya dauki hayar wani mutum mai suna Dhamdhamu bn Amru Alghifariy ya turashi zuwa garin Makkah cewa yaje ya sanar da Quraishawa cewa ga ANNABI MUHAMMADU nan (saww) ya fito domin ya tare musu ayarin kasuwancinsu.

Da yaje Makkah, ya hau kan wani dutse daga cikin duwatsun garin sannan ya yayyaga tufafinsa, ya rika kwarara eehu yana kiran sunayen manyan kafiran makkah yana vasu labarin halin da ake ciki.

Don haka gaba dayan kafiran nan na Makkah sai tsohuwar Qiyayyar da suke ma Annabi (saww) da sahabbansa ta motsa musu. Suka tashi suka daura shirin yaki suka fito.

Dukkan Manyan garin Makkah babu wanda bai fito wannan yakin ba, in banda Abu Lahab (L. A). shima sai da ya turo Al-aas bn Hisham domin ya wakilceshi awajen Yaqin...

DAGA ZAUREN FIQHU.

Ya Allah yi salati ga Annabi Muhammadu gwargwadon kulawarka da sha'aninsa aranar Badar da sauran Yakokinsa.  Wa aalihi wa sahbihi wa sallim.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI