QARFIN RUNDUNAR KAFIRAI
Adadin dakarun Mushrikan Makkah wadanda suka fito yakin badar, Su dubu daya ne (1,000).
Acikinsu akwai mutum dari shida (600) suna tafiya a Qasa, suna sanye da Sulke da kwakwali da sauran kayan yaki.
Sannan akwai mutum dari akan dawakai, su ma suna sanye da cikakken shirin kayan yaki. Kuma akwai Rakumma guda dari bakwai (700) tare dasu akwai Zabiyoyi (irin fitsararrun matan nan masu rera musu wakkoki na habaici ga Musulmai).
Kwamandan dake rike da tutar kafirai awannan ranar shine ASSA'IBU BN YAZEED (sannan bai Musulunta ba). ya musulunta daga baya, kuma shine Kakan na biyar ga Imamush Shafi'iy (rah).
Mutum goma sha biyu ne suka dauki nauyin ciyar da Sojojin rundunar. sune kamar haka:
1. Abu Jahal (L. A).
2. Utbatu bn Rabee'ah. (L. A).
3. Shaibatu bn Rabee'ah (L. A)
4. hakeem bn Hizaam.
5. Al-Abbas bn Abdil Muttalib.
6. Abul Bakhtariy.
7. Zam'atu bn Aswad.
8. Ubayyu bn Khalaf (L. A).
9. Umayyatu bn Khalaf (L. A).
10. An-Nadhru bn Alharith.
11. Nabeehu bn Alhajjaj.
12. Munabbihu bn Alhajjaj.
Kowanne daga cikinsu yana yanka rakumma guda goma sha biyu ne a kullum. Kuma akansu ne Allah ya saukar da ayar nan ta 36 acikin Suratul Anfaal:
"WADANNAN DA SUKA KAFIRTA SUNA CIYAR DA DUKIYARSU DOMIN SU TOSHE (MUTANE) DAGA BIN HANYAR ALLAH, DA SANNU ZASU CIYAR DA ITA (DUKIYAR) SANNAN ZATA ZAMA ASARA AKANSU, SANNAN ZA'AYI RINJAYE AKANSU".
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP.
Ya Allah yi salati da tasleemi ga Ma'aikinka da iyalan gidansa adadin dukkan wadanda suka taba yin salati agareshi, harma wadanda basu taba yi ba.
Comments
Post a Comment