QARFIN RUNDUNAR MUSULMAI

Duk gaba dayan wadanda suka fito tare da Manzon Allah (saww) mutum dari uku ne da sha uku (313). Ance lokacin D Manzon Allah (saww) ya Qirgasu yaga adadinsu yayi farinciki. harma ya gaya musu cewa wannan adadin shine adadin yawan Mutanen da Suke cikin rundunar 'DALUTU wadanda suka tsallake Qoram tare dashi. (wadanda Allah ya bada labarinsu acikin Suratul Baqarah).

Sun tahi tare da Rakumma guda SABA'IN, dawakai kuma guda biyu Rak!!. Doki daya na Miqdadu bn Amru ne. Dayan kuma na Marthad bn Abi Marthad Alganawiy (ra).

Babbar tutar yakin tana hannun MUS'ABU BN UMAIR. Amma akwai wasu Qananan tutocin Bakake guda biyu agaban Manzon Allah (saww). Daya tana hannun Aliyu bn Abi Talib (ra), dayar kuma tana hannun wani daga cikin mutanen Madinah.

Daga chan Qarshen bayan rundunar kuma, akwai wani Sadaukin Sahabi mai suna Qaysu bn Sa'asa'ah Al-Ansariy (ra).

Idan an dubi yadda rundunonin guda biyu suke, za'a ga cewa rundunar kafiran ta ninka yawan rundunar musulman har sau uku. Kuma sun fisu yawan makamai da kuma cikakken shirin yakin.

Sai dai Kuma nasara ahannun Allah take. Shi ke bayarwa ga wanda yaso.

DAGA ZAUREN FIQHU.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI