MAGANARSA DA DABBOBI (SAWW) 07
Alqadhy 'Iyadh bn Musa Alyahsubiy (Allah ya rahamsheshi) ya ruwaito acikin littafinsa Mai albarka (Ash-Shifa) aciki Qissar makiyayin dabbobin nan wanda kura tayi magana dashi, mutumin yana cikin tsananin mamaki sai kurar tace masa "Ai kai ne babban abun mamaki.. Kana tsaye akan tumakinka kuma ka bar wannan Annabin wanda Allah bai ta'ba aiko Annabin da ya fishi girma ba (baka je ka bada gaskiya dashi ba).
"Kuma yana da daraja awajen Allah tunda har an bude masa Qofofin Aljannah kuma ga 'Yan Aljannar nan an bude musu suna kallon Yaqin Sahabbansa. Babu abinda ke tsakaninka dashi sai wannan Surkukin. (Kaje kayi imani dashi) Sai kaima ka zamto acikin rundunar Allah".
Sai shi Makiyayin yace mata "To wa zai kula min da tumaki na?".
Sai tace "Ni zan kula maka dasu har sai ka dawo".
Sai ya sallamar da dabobinsa ga Kurar, kuma ya tafi yaje ya tarar da Manzon Allah (saww) awajen Yaqi, ya bashi labarin dukkan avidna ya faru tsakaninsa da kurar, kuma ya Musulunta.
Sai Manzon Allah (saww) yace masa "Koma zuwa ga tumakinka zaka samesu kamar yadda suke". Yaje kuwa ya gansu haka din, sai ya yanka ma kurar nan akuya guda daga cikin garken.
Salatin Allah da amincinsa da albarkokinsa adadin yardar Allah da gudanuwar ikonsa su tabbata bisa Annabi Muhammadu da iyalan gidansa da Sahabbansa da mabiyansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (04/12/1439 15/08/2018).
Comments
Post a Comment