Posts

Showing posts from August, 2018

MAGANARSA DA DABBOBI (SAWW) 07

Alqadhy 'Iyadh bn Musa Alyahsubiy (Allah ya rahamsheshi) ya ruwaito acikin littafinsa Mai albarka (Ash-Shifa) aciki Qissar makiyayin dabbobin nan wanda kura tayi magana dashi, mutumin yana cikin tsananin mamaki sai kurar tace masa "Ai kai ne babban abun mamaki.. Kana tsaye akan tumakinka kuma ka bar wannan Annabin wanda Allah bai ta'ba aiko Annabin da ya fishi girma ba (baka je ka bada gaskiya dashi ba). "Kuma yana da daraja awajen Allah tunda har an bude masa Qofofin Aljannah kuma ga 'Yan Aljannar nan an bude musu suna kallon Yaqin Sahabbansa. Babu abinda ke tsakaninka dashi sai wannan Surkukin. (Kaje kayi imani dashi) Sai kaima ka zamto acikin rundunar Allah". Sai shi Makiyayin yace mata "To wa zai kula min da tumaki na?". Sai tace "Ni zan kula maka dasu har sai ka dawo". Sai ya sallamar da dabobinsa ga Kurar, kuma ya tafi yaje ya tarar da Manzon Allah (saww) awajen Yaqi, ya bashi labarin dukkan avidna ya faru tsakaninsa da kurar, ku

MAGANIN CHUTUKAN FATA :

TAMBAYA TA 2554 ******************* Assalamu Alaikum malam ya iyali? ya hakuri da jama'a?  Ubangji Allah ya saka da gidan aljanna, don Allah malam magani nikeso ataimaka mani dashi, wanda ya danganci fata, wata irin cutace nike fama da ita shidai ba makero ba amma azababben kaikayi gareshi idan ina sosashi sai yayi bororo ya fashe kamar wuta ,wani lokaci ma har jini yake idan ina sosawa nasa magunguna da dama amma haryanzu sai dai sauki, kuma da ga kafafu da hannu ne kadai amma yanxu ya bulla har ga jiki.Bissalam. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Daga cikim jerin magungunan Musulunci wadanda ake magance irin wadannan chutukan dasu akwai : - Man Jirjir, - Man kwakwa. - Man Ghelo. - Man Kadanya. - Man Alayyadi. - Man Zaitun. - Man Aloe Vera. Shin Man Zaitun ana amfani dashi akan matsalolin fata wadanda basuyi zurfi ba. Saboda shi bashi da zafi. Amma idan abu yadan yi nisa sai kiyi amfani da sauran, daya bayan daya. Ko kuma ki hadasu waje gud

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (106)

2 DAUKAR HAJJI DAGA MASALLACIN QUDUS ********************************************* hadisi daga Yahya bn Abi Sufyan Al-Akhnasiy, daga Kakarsa Hakeematu daga Ummu Salamah matar Manzon Allah (saww) tace taji Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yana cewa : "Duk wanda ya dauko niyyar aikin hajji ko umrah daga Masallaci mafi nisa (wato masallacin Kudus) zuwa ga Masallaci mai alfarma (Masallacin Ka'abah) to Allah zai gafarta masa abinda ya gabata da kuma abinda ya jinkirta daga zunubansa, ko kuma Aljannah ta wajabta gareshi. (daya daga cikin mazajen hadisin ne yayi kokwanton ainahin kalmar da aka fa'da). Abu Dawud ne ya ruwaito hadisin acikin Sunanu nasa, Juzu'i na 2 shafi na 143. Kuma yace "Allah ya jiqan Malam Wakee'u (Malamin su Imam Shafi'iy) yayi harramar hajji daga Masallacin Qudus zuwa Makkah. QARIN BAYANI *************** Wannan falala ce ta musamman wacce ta kebanci mazaunan birnin Qudus da sauran biranen dake kewaye dashi, sai ku

MAGANIN CHUTUKAN FATA :

TAMBAYA TA 2554 ******************* Assalamu Alaikum malam ya iyali? ya hakuri da jama'a?  Ubangji Allah ya saka da gidan aljanna, don Allah malam magani nikeso ataimaka mani dashi, wanda ya danganci fata, wata irin cutace nike fama da ita shidai ba makero ba amma azababben kaikayi gareshi idan ina sosashi sai yayi bororo ya fashe kamar wuta ,wani lokaci ma har jini yake idan ina sosawa nasa magunguna da dama amma haryanzu sai dai sauki, kuma da ga kafafu da hannu ne kadai amma yanxu ya bulla har ga jiki.Bissalam. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Daga cikim jerin magungunan Musulunci wadanda ake magance irin wadannan chutukan dasu akwai : - Man Jirjir, - Man kwakwa. - Man Ghelo. - Man Kadanya. - Man Alayyadi. - Man Zaitun. - Man Aloe Vera. Shin Man Zaitun ana amfani dashi akan matsalolin fata wadanda basuyi zurfi ba. Saboda shi bashi da zafi. Amma idan abu yadan yi nisa sai kiyi amfani da sauran, daya bayan daya. Ko kuma ki hadasu waje gud

SHAUKIN SON MA'AIKI (SAWW) DAGA KUTUTTUREN DABINO

Image
Acikin jerin Mu'ujizozin Manzon Allah (saww) wadanda Zauren Fiqhu ke kawowa, in sha Allahu yau zamuyi magana akan Shahararriyar Mu'ujizar nan wacce duniya take labari. Wato Kukan da itacen dabino (Kututture) yayi saboda shauki, da kuma tashin hankalin da yaji yayin rabuwa da Ma'aiki (saww). Hadisi daga Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (ra) yace : Manzon Allah (saww) ya kasance ranar Juma'a yana tsayawa ajikin wata bishiya ko itacen dabino (Idan zai yi Khutbah). Sai wata Mace ko Namiji daga cikin mutanen Madeenah tace "Ya Rasulallahi ko mu sanya maka Mimbari ne?". Sai Manzon Allah (saww) yace: "IDAN KUN SO". Don haka sai suka sanya masa Minbari. Yayin da ranar Juma'a tayi, Manzon Allah (saww) ya tafi zuwa ga Minbarin, Sai wannan itacen dabinon yayi kururuwa irin Kururuwar da Jariri ke yi. Sai Manzon Allah (saww) ya sauko (daga kan Minbarin) yaje ya rungumeshi. Sai ya rika yi wani abu kamar yadda yaro Qarami keyi idan an rarrasheshi. Sai

MAGANIN CHUTUKAN FATA :

TAMBAYA TA 2554 ******************* Assalamu Alaikum malam ya iyali? ya hakuri da jama'a?  Ubangji Allah ya saka da gidan aljanna, don Allah malam magani nikeso ataimaka mani dashi, wanda ya danganci fata, wata irin cutace nike fama da ita shidai ba makero ba amma azababben kaikayi gareshi idan ina sosashi sai yayi bororo ya fashe kamar wuta ,wani lokaci ma har jini yake idan ina sosawa nasa magunguna da dama amma haryanzu sai dai sauki, kuma da ga kafafu da hannu ne kadai amma yanxu ya bulla har ga jiki.Bissalam. AMSA ******* Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Daga cikim jerin magungunan Musulunci wadanda ake magance irin wadannan chutukan dasu akwai : - Man Jirjir, - Man kwakwa. - Man Ghelo. - Man Kadanya. - Man Alayyadi. - Man Zaitun. - Man Aloe Vera. Shin Man Zaitun ana amfani dashi akan matsalolin fata wadanda basuyi zurfi ba. Saboda shi bashi da zafi. Amma idan abu yadan yi nisa sai kiyi amfani da sauran, daya bayan daya. Ko kuma ki hadasu waje gud

SHIN WANENE ANNAMIMI? 02

Assalamu alaikum Jama'a, wannan shine kashi na biyu acikin wani darasin da yazo muku daga Zauren Fiqhu Whatsapp, mai irin wannan sunan. Gashi nan zamu ci gaba daga inda muka tsaya kamar haka : Malamai suka ce bayyanar da sirrukan jama'a awajen da bai kamata a bayyanar dashi ba, shima yana daga cikin annamimanci kuma haramun ne. 'Yan uwa ku sani cewa kowanne Musulmi mumini yana da wata alfarma ta musamman awajen wacce bai halatta aketa masa ita ba, sai ko akan wani hakki na shari'ah. Sayyiduna Abdullahi bn Umar (rta) yace "Naga Manzon Allah (saww) yana dawafi adakin ka'abah yana cewa "MAMAKIN TSARKINKI!  DA TSARKIN QAMSHINKI!. MAMAKIN GIRMANKI, DA GIRMAN ALFARMARKI!. AMMA INA RANTSUWA DA WANDA RAN ANNABI MUHAMMADU (SAWW) KE KARKASHIN IKONSA, WALLAHI ALFARMAR MUMINI TAFI GIRMA AWAJEN ALLAH FIYE DAKE. DUKIYARSA (SHI MUMININ) DA JININSA, KUMA KADA AYI MASA WANI ZATO SAI NA ALLHAIRI". (Ibnu Maajah ne ya ruwaitoshi). Kowanne Musulmi yana da alfarma ta

NAU'O'IN AZABAR QABARI (02)

Idan ba'a manta ba, tun kwanakin baya Anan Zauren Fiqhu mun kawo muku farkon wannan darasin kashi na daya zuwa na uku. Yanzu kuma ga na hudu : Nau'in azabar Qabari na hudu shine MATSEWAR QABARI. Wato Qabarin zai matse wanda ke cikinsa, Matsewa mai tsanani wanda har sai Qasusuwan haqarkarinsa sun shige cikin junansu...!! Ita wannan matsewar tana faruwa akan kowa. Musui ko kafiri. Kamar yadda Hadisai masu yawa suka bayyana. Misali kamar hadisin da Khalal ya karbo da isnadinsa zuwa ga Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa (game da kafiri) : "QABARIN ZAI MATSESHI HAR SAI RUWAN KWAKWALWARSA YA RIKA FITA TA TSAKANIN FARATUNSA DA NAMAN JIKINSA". Akwai hujjoji da yawa da suke tabbatar da cewa lallai wannan matsewar tana shafar Mumini da kafiri. Kamar yadda Malamai da yawa suka bayyanar. Misali kaae ibnu Battah da waninsa. Ga kuma hadisin da Shu'ubah ya karbo daga Sa'adu 'dan Ibrahim daga Nafi'u daga Nana A'ishah (ra) ita k

NAU'O'IN AZABAR QABARI (01)

Da sunan Allah Mabuwayin Sarki Gagara-Misali. Wanda ya halicci 'Yan Adam daga Qasa, Kuma ya sanyata ta zama Makwancinsu bayan rasuwarsu, sannan kuma daga cikinta zai tashesu aranar babban taro. Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da Allah ya zabeshi ya fifita Halittar jikinsa da halayensa da nasabarsa fiye da na sauran halittunsa baki daya, tare da iyalan gidansa da Sahabbansa Taurarin Shiriya. Bayan haka, kamar yadda daliban Zauren Fiqhu suka sani, mun sha kawowa ayoyi, hadisai da hikayoyi wadanda suke tabbatar da cewa azabar Qabari gaskiya ce. Harma mun kawo zancen da Qabari ke yi yayin da za'a sanya Ma'abocinsa cikinsa. Yau kuma in sha Allah zamuyi magana ce akan kala-kalar azabobin Qabari da kuma yadda suke gudana. Kamar yadda muka sha gaya muku acikin darussan Zauren Fiqhu da suka gabata, ita dai azabar Qabari tana gudana ne akan jiki da ruhin Bil Adam. Ga nau'o'inta nan kamar haka : 1. DUKA DA GUDUMAR BAQIN QARFE : Akwai ruwayoyi daban-daban ta hanyo

IMAM MUHAMMADUL BAQIR (RTA)

Yau ma muna tare da wani jigo ne daga jiga-jigan al'ummar gidan Annabta (Ahlul Baiti). Sunansa Muhammad, irin sunan Kakansa na farko kenan (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Sunan Mahaifinsa Aliyu bn Alhusain wanda ake yiwa laqabi da Zainul Abideena. Mahaifiyarsa ita ce Ummu Abdillahi, Fatimah 'yar Imamul Hasan Almujtabah (amincin Allah ya tabbata garesu da dukkan Ahlul Baiti baki daya) . Ana yi masa Alkunya da Abu Ja'afar  (saboda 'dansa Ja'afarus Sadiq). Kuma saboda zurfin iliminsa ana yi masa laqabi da "BAQIRUL ULUM" (Mai yalwar Ilimi, mai tsage Ilimai, rumbun ilimai). An haifeshi aranar Talata 3 ga watan Safar shekara  ta 57 bayan Hijirar Kakansa (Sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Shekarunsa uku aduniya lokacin da aka shahadantar da Kakansa Imamul Husaini (yardar Allah ta tabbata garesu baki daya). Ya rasu kuma aranar 23 ga watan Safar shekara ta 114 bayan Hijira.  Wasu kuma sun ce ya rasu ne ashekara ta 117. Wasu kuma sun ce shek

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (11)

Da Sunan Allah Rayayyen Sarkin da gyangyadi bai ta'ba riskarsa ba, balle barci. Salati da aminci su tabbata bisa Ma'abocin Farkon Zance aranar da dukiya da 'ya'ya basu amfani, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa Gwargwadon girmansa. Hakika lamarin Alqiyamah da girma yake.. Babu mai tsallake firgicinta sai wadanda Allah ya za'ba daga cikin bayinsa. Yayin da Mala'ika Israfeelu yayi busar farko acikin Qaho, dukkan mutane basu firgita su dimauce da eehu tamkar mashayan dake tambele.  Kuma wannan firgitar da tashin hankalin da sumewar bata kebanci 'yan Adam kadai ba. Domin kuwa Allah cewa yayi : "RANAR DA ZA'AYI BUSA ACIKIN QAHO SAI DUKKAN WADANDA KE CIKIN SAMMAI DA WADANDA KE CIKIN QASSAI SU FIRGICE, SAI DAI WADANDA ALLAH YASO... " Wato wannan firgitar zata shafi kowa da kowa. Daga nan sai kuma mutuwa ta riskesu baki daya. Ibnu Hajr Al Asqalaniy (rah) yace "Busa ne guda biyu - ta farkon acikinta ne duk masu m

RANAR DA ZA'A YANKA MUTUWA!!

Aranar Alkiyamah za'a zo da Mutuwa bisa siffar rago kosasshe. Sai wani mai kira yayi kira yace "Ya ku 'Yan Aljannah!". Sai su 'daga kansu suna kallo. Sai a tambayesu "Shin kun san wannan?". Sai suce "Eh ai mutuwa ce". Da yake dukkansu sun ta'ba ganinta. Sannan ache "Ya ku 'Yan wuta!". Sai su 'chira kansu suna kallo, Sai ache musu "shin kun san wannan?". Sai suce "Eh ai mutuwa ce" Da yake dukkansu sun ta'ba ganinta. Nan take za'a yankata, Sannan ache "Ya Ku 'Yan Aljannah! Zaku dawwama ne acikinta babu mutuwa. Kuma Ya Ku 'yan witay, Dawwama zakuyi acikinta babu mutuwa". Acikin wata riwayar aka ce "Sai 'Yan Aljannah su Qara farin ciki bisa farin cikinsu, Kuma 'Yan wuta su Qara bakin ciki bisa bakin cikinsu. (BUKHARIY DA MUSLIM). YA ALLAH KA SANYAMU A ALJANNARKA KA KIYAYEMU DAGA WUTA. AMEEN. DAGA ZAUREN FIQHU (06-08-2018 24/11/1439).

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (103)

MUTUWA A KARSHEN RAMADHAN ************************************ Khaysamah bn AbdirRahman ya karbo hadisi ta hanyar Sayyiduna Abdullahi bn Mas'ud (radhiyallahu anhu) yace "Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace : "DUK WANDA MUTUWARSA TA DACE DA QARSHEN RAMADHAN ZAI SHIGA ALJANNAH". ADUBA : - Zaylut Taqyeed juzu'i na 1 shafi na 233. QARIN BAYANI *************** Hakika Ramadhan yana kunshe da alkhairai masu yawa. Kuma idan karshensa yazo Allah yana ninninka adadin bayinsa masu samun babban rabo awajensa. Daga cikin irin babban rabon da bayin Allah Muminai ke samu, duk wanda ya rasu a karshen watan Ramadhan to Allah zai sanyashi cikin Aljannarsa. Ya Allah ka gafarta mana laifukanmu ka kyautata karshenmu kasa mu cika da Imani ameen. DAGA ZAUREN FIQHU (04/08/2018  22/11/1439).

DAGA TASKAR AHLUL BAITI (ALAIHIMUS SALAM)

IMAM JA'AFAR ASSADIQ (RTA) YACE: "Ina mamakin mutumin da yake cikin tsoro amma bai dukufa cikin karanta "HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL" ba. Ina mamakin mutumin da Bakin ciki ya dameshi amma bai karanta "LA ILAHA ILLA ANTA SUB'HANAKA INNEE KUNTU MINAZ ZWALIMEENA" ba. "Ina mamakin Mutumin da Masu Makirci suka dameshi da Makirci amma bai karanta "WA UFAWWIDHU AMREE ILAL LAAH. INNAL LAAHA BASEERUN BIL 'IBAADI' ba". Ni kuma Mai Zauren Fiqhu na Qara da cewa : "Ina mamakin mutumin da yake fama da wata jinya ko rashin lafiya, amma bai yawaita karanta "ANNEE MASSANIYADH DHURRU WA ANTA ARHAMUR RAHIMEENA' ba". "Ina mamakin mutumin da yake neman haihuwa amma bai yawaita "RABBEE HABLEE MIN LADUNKA DHURRIYYATAN TAYYIBAH, INNAKA SAMI'UD DU'A'I ba". "Ina mamakin mutumin da talauci ya dameshi amma bai yawaita Istighfari da Salatin Annabi (saww) ba. Ina mamakin mutumin da ya shiga mats

SHIN WANENE ANNAMIMI? (01)

Annamimanci yana daga cikin miyagun ayyuka ko halayen da Allah ya haramtasu bisa bayinsa muminai. Domin yana iya wargaza hadin kai da haddasa Qiyayya atsakanin al'ummah. Annamimanci yana daga cikin halayen 'Yan wuta, Kuma shi reshe ne daga rassan munafurci. Kuma Allah yayi alkawarin cewa mai yinsa ba zai shiga Aljannah ba. Annamimanci yna janyo ma masu yinsa su samu tsananin azabar Qabari wacce bata da Misali, Kamar yadda Manzon Tsira (saww) ya bayyana acikin hadisai da dama. (Allah shi kiyayemu). ANNAMIMANCI : Shine daukar magana daga wajen wani ko wasu da kuma isar da ita zuwa ga wani ko wasu, da niyyar haddasa husuma atsakanin Jama'a. Duk mai yin haka shine Annamimi kuma shine Munafuki.. Malamai sun ce ANNAMIMAI kala biyu ne kamar haka : NAMMAM : Shine Qaramin Annamimi wanda za'ayi magana yana wajen, koda ba'a gayyaceshi ba. Ko kuma an yarda dashi anyi maganar agabansa, sannan ya dauka ya kaima wasu don neman shiga awajensu, ko kuma don haddasa fitina atsaka

IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (13)

DA SUNAN ALLAH RAYAYYEN DAKE RAYA DUKKAN MATATTU. Salati da amincin Allah su tabbata bisa Annabin da yazo da hasken dake raya zukata, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan mabiyansu da kyautatawa har zuwa ranar da Jarirai ke fidda furfura. Wannan ita ce fitowa ta goma sha uku acikin darasin Zauren Fiqhu wanda ke dauke da labarin tashin Alqiyamah da nauye-nauyenta. Tsakanin busa ta farko da ta biyu tsawon shekaru arba'in ne. Sannan Allah zai sanya sararin samaniya tayi wani irin ruwa mai kama da maniyyin mazaje, wanda daga gareshi ne za'a sake gina halittar jikkunan halittu. Zasu rika tsirowa daga Qasa kamar yadda shuka ke tsirowa. Dama tun lokacin da jikkunan mutane suka narke suka zama Qasa, akwai wani Qashi wanda ba ya narkewa. Wato Qashin gadon baya (Vitabrae) to daga gareshi ne sauran Qasusuwa zasu tsira, sai kuma halittar jiki ta ginu, sai kuma jiran lokacin da Qasar zata tsage ta fidda nauye-nauyen dake cikinta.. Allahu Akbar!! B

YA ALLAH ABIN DOGARO ABIN NEMA

Ya Allah lallai duk wanda ya samu girma dominka ba zai Qaskanta ba. Domin kai ne AL-AZEEZU Mabuwayin da ba ya Qaskanta, kuma babi mai iya rinjayarsa. Ya Allah duk wanda ya shiryu da kai ba zai 'bata ba. Domin kai ne ALHADIY, Mai shiryar da bayinsa ta yadda yaso. Ya Allah lallai duk wanda ya yalwatu da kai, ba zai samu Qaranta ba. Domin kai ne ALWASI'U. Mai yalwar da babu Qarewa. Ya Allah lallai duk wanda ya Qarfafa dakai ba zai raunana ba. Domin Kai ne ALQWIYYU Mai Qarfin da ba ya rauni ba ya gajiyawa. Ya Allah lallai duk wanda ya Wadatu da Kai ba zai bukatu ga waninka ba. Domin kai ne ALGANIYYU.  Mawadacin da ba ya talauta. Kuma taskarsa ba ta Qarewa. Duk wanda ya Dogara da kai ba zai ta'be ba. Duk wanda ya zamanto Kai ne Mafakarsa to ba zai tozarta ba. Kuma duk wanda yayi riko da kai to lallai hakika ya shiryu zuwa ga Tafarki Madaidaici. Ya Allah don Qarfin ikonka ka isar mana akan duk wanda ya zaluncemu. Ka kiyayemu daga kaidin Makiya da Mahassada. Don buwayar Qa

KWARJININ MANZON ALLAH (SAWW)

Annabi (saww) shine mafi kyawu mafi kwarjini acikin dukkan bayin Allah. Wannan kwarjinin nasa shine ya lullube kyawun. Shi yasa Mutane basu fitinu da kyawunsa kamar yadda ya faru ga Annabi Yusuf (as) ba. Manyan Sahabbansa irin su Sayyiduna Abubakar da Umar (ra) basu iya bayanin siffofinsa sosai saboda kwarjininsa ya hana su Qare masa kallo. Idan Suna zaune agabansa, dukkaninsu sukan sunkuyar da kansu Qasa ne. Basu iya cira kai su kalleshi, basu yin surutu ko hayaniya atsakaninsu. Hasali ma basu iya yin magana har sai in bukatar hakan ta taso. Sayyiduna 'Amru bn Al-Aas (ra) yace "Idan muka zauna agaban Manzon Allah (saww) mukan shiga cikin wasu irin yanayi guda biyu masu girma : - Yanayi na farko shine muna son mu 'daga kai mu kalleshi saboda tsananin Soyayyarmu gareshi da kuma farin cikin kasancewa tare dashi. - Yanayi na biyu kuma, Kwarjininsa yakan lullubemu har sai munji ba zamu iya yin koda motsi agabansa ba.  (saww). Hakika na zauna agabansa sau da yawa. Amma wal