HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (103)

MUTUWA A KARSHEN RAMADHAN
************************************
Khaysamah bn AbdirRahman ya karbo hadisi ta hanyar Sayyiduna Abdullahi bn Mas'ud (radhiyallahu anhu) yace "Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace :

"DUK WANDA MUTUWARSA TA DACE DA QARSHEN RAMADHAN ZAI SHIGA ALJANNAH".

ADUBA :

- Zaylut Taqyeed juzu'i na 1 shafi na 233.

QARIN BAYANI
***************
Hakika Ramadhan yana kunshe da alkhairai masu yawa. Kuma idan karshensa yazo Allah yana ninninka adadin bayinsa masu samun babban rabo awajensa.

Daga cikin irin babban rabon da bayin Allah Muminai ke samu, duk wanda ya rasu a karshen watan Ramadhan to Allah zai sanyashi cikin Aljannarsa.

Ya Allah ka gafarta mana laifukanmu ka kyautata karshenmu kasa mu cika da Imani ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU (04/08/2018  22/11/1439).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI