RANAR DA ZA'A YANKA MUTUWA!!

Aranar Alkiyamah za'a zo da Mutuwa bisa siffar rago kosasshe. Sai wani mai kira yayi kira yace "Ya ku 'Yan Aljannah!".

Sai su 'daga kansu suna kallo. Sai a tambayesu "Shin kun san wannan?".

Sai suce "Eh ai mutuwa ce". Da yake dukkansu sun ta'ba ganinta.

Sannan ache "Ya ku 'Yan wuta!". Sai su 'chira kansu suna kallo, Sai ache musu "shin kun san wannan?".

Sai suce "Eh ai mutuwa ce" Da yake dukkansu sun ta'ba ganinta.

Nan take za'a yankata, Sannan ache "Ya Ku 'Yan Aljannah! Zaku dawwama ne acikinta babu mutuwa. Kuma Ya Ku 'yan witay, Dawwama zakuyi acikinta babu mutuwa".

Acikin wata riwayar aka ce "Sai 'Yan Aljannah su Qara farin ciki bisa farin cikinsu, Kuma 'Yan wuta su Qara bakin ciki bisa bakin cikinsu.

(BUKHARIY DA MUSLIM).

YA ALLAH KA SANYAMU A ALJANNARKA KA KIYAYEMU DAGA WUTA. AMEEN.

DAGA ZAUREN FIQHU (06-08-2018 24/11/1439).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI