IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (11)

Da Sunan Allah Rayayyen Sarkin da gyangyadi bai ta'ba riskarsa ba, balle barci. Salati da aminci su tabbata bisa Ma'abocin Farkon Zance aranar da dukiya da 'ya'ya basu amfani, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa Gwargwadon girmansa.

Hakika lamarin Alqiyamah da girma yake.. Babu mai tsallake firgicinta sai wadanda Allah ya za'ba daga cikin bayinsa.

Yayin da Mala'ika Israfeelu yayi busar farko acikin Qaho, dukkan mutane basu firgita su dimauce da eehu tamkar mashayan dake tambele.  Kuma wannan firgitar da tashin hankalin da sumewar bata kebanci 'yan Adam kadai ba. Domin kuwa Allah cewa yayi :

"RANAR DA ZA'AYI BUSA ACIKIN QAHO SAI DUKKAN WADANDA KE CIKIN SAMMAI DA WADANDA KE CIKIN QASSAI SU FIRGICE, SAI DAI WADANDA ALLAH YASO... "

Wato wannan firgitar zata shafi kowa da kowa. Daga nan sai kuma mutuwa ta riskesu baki daya.

Ibnu Hajr Al Asqalaniy (rah) yace "Busa ne guda biyu - ta farkon acikinta ne duk masu mutuwa zasu mutu. Wadanda Allah ya kebancesu kuma zasu suma. Idan anyi busar Qaho ta biyu kuma acikinta ne kowanne matacce zai tashi, Kuma kowanne sumamme zai farfado".

Ubangiji ya buga misali da Jarirai har sau uku game da girman tashin hankalin Alqiyamah. Ya siffata mana ita kamar haka :

- Ranar da zaku ganta, Kowacce mai shayarwa zata jefar da abinda take shayarwa.

- Ranar da Mai ciki zata haife abinda take dauke dashi.

- Ranar dake sanya jarirai yin furfura.

Duk wanda yake so yaga yadda Alqiyamah zata kasance kamar akan idonsa, to ya karanta surorin nan guda uku :

- Idhash Shamsu kuwwirat. (Suratut Takweer).

- Idhas Sama'un Fatarat (Suratul Infitaar).

- Idhas Sama'un Shaqqat (Suratul Inshiqaq).

Abubuwan dake gabanmu yanzu anan duniya sune kamar haka :

- Sararin samaniya.
- Qasa.
- Duwatsu.
- Tekuna.
- Dabbobi.
- Rana, Wata da Turari.

To dukkan wadannan abubuwan Allah ya bamu labarin yadda makomarsu zata kasance aranar Alqiyamah.

SAMMAI : Allah yace "Idan sama aka kyeceta".

QASSAI : "Idan aka girgiza Qasa mutukar girgizawarta, Kuma Qasa ta fitar da nauye-nauyenta".

DUWATSU : "Ranar da za'a nike Qasa da duwatsu".

"Kuma duwatsu zasu zamanto tamkar gashin buzun da aka jeme".

TEKU : Allah yace "Kuma idan tekuna suka kyakkece (Suka hade da junansu).

"Idan tekuna aka cinna wuta garesu".

Wato zasu hade da junansu kuma daga karshe Ubangiji zai sa su kama da wuta baki dayansu.. (SUBHANALLAH).

DABBOBI : "Idan dabbobi aka tashesu (Domin yin hisabi atsakaninsu)

RANA DA TAURARI : "Idan rana aka tafiyar da haskenta, Idan Taurari aka gurbacesu (wato launinsu ya chanza, suka gauraye da junansu).

Ibnu Abi Hatam ya ruwaito hadisi ta hanyar Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) yana cewa "Rana da Wata da Taurari  Allah zai dulmiyar dasu acikin Teku ne aranar Alqiyamah sannan ya aiko da wata iska mai Qarfi wacce zata cinna musu wuta".

Wannan kenan daga abubuwan da duk wani mai rai awannan lokacin sai ya gani da idonsa idan lokaci yayi.

Ya Allah kasa mu cika da imani ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU (22/08/1439  07/05/2018).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI