SHIN WANENE ANNAMIMI? (01)

Annamimanci yana daga cikin miyagun ayyuka ko halayen da Allah ya haramtasu bisa bayinsa muminai. Domin yana iya wargaza hadin kai da haddasa Qiyayya atsakanin al'ummah.

Annamimanci yana daga cikin halayen 'Yan wuta, Kuma shi reshe ne daga rassan munafurci. Kuma Allah yayi alkawarin cewa mai yinsa ba zai shiga Aljannah ba.

Annamimanci yna janyo ma masu yinsa su samu tsananin azabar Qabari wacce bata da Misali, Kamar yadda Manzon Tsira (saww) ya bayyana acikin hadisai da dama. (Allah shi kiyayemu).

ANNAMIMANCI : Shine daukar magana daga wajen wani ko wasu da kuma isar da ita zuwa ga wani ko wasu, da niyyar haddasa husuma atsakanin Jama'a. Duk mai yin haka shine Annamimi kuma shine Munafuki..

Malamai sun ce ANNAMIMAI kala biyu ne kamar haka :

NAMMAM : Shine Qaramin Annamimi wanda za'ayi magana yana wajen, koda ba'a gayyaceshi ba. Ko kuma an yarda dashi anyi maganar agabansa, sannan ya dauka ya kaima wasu don neman shiga awajensu, ko kuma don haddasa fitina atsakanin jama'a.

QATTAT : Shine Babban Annamimi Kwararre wanda duk sanda yaga alamar wasu suna ganawa sai ya la'be yana jinm zancensu ba tare da saninsu ba, sannan ya dauka ya kaima wani ko wasu. Ko kuma ya dauko labarai marassa tushe sannan ya rika watsawa atsakanin jama'a don zubda Mutuncin wani ko wata ko wasu. Masu irin wannan halin suna daga cikin mafiya sharrin halittu adoron Qasa..

Imamul Ghazali (Allah ya rahamsheshi) yace "Ainahin Qarshen ma'anar Annamimanci shine bayyanar da abinda ba'a son bayyanarsa. Koda wanda aka dauko zancen daga wajensa ba yaso, ko kuma shi wanda aka gaya ma zancen ne ba yaso. Koda wannan tonon asirin an yishi ne ta hanyar yin furuci da wasu alamomi, ko arubuce, ko kuma da isharah.

Yaci gaba da cewa "Hakikar Annamimanci shine shine tonon asiri, da keta mutunci daga abinda ba'a son bayyanar dashi. Koda kudi ka gani awajen wani dan uwanka yana kokarin boyewa sai ka bayyanar dashi to kayi annamimanci kenan.

Ina jan hankalin masu yin rubuce-rubuce a jaridu da Social Media cewa arika kiyayewa kada mutum ya tsinci kansa acikin Annamimai aranar mutuwarsa da kuma ranar hisabi.

Anan zamu tsaya, sai arubutu na biyu zamu ji irin mummunan sakamakon da Annamimai zasu tarar a lahira.

AN GABATAR DA KARATUN A ZAUREN FIQHU WHATSAPP RANAR LARABA 25/07/2018 12/11/1439.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI