IDAN ALQIYAMAH TA TSAYA (13)

DA SUNAN ALLAH RAYAYYEN DAKE RAYA DUKKAN MATATTU.

Salati da amincin Allah su tabbata bisa Annabin da yazo da hasken dake raya zukata, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan mabiyansu da kyautatawa har zuwa ranar da Jarirai ke fidda furfura.

Wannan ita ce fitowa ta goma sha uku acikin darasin Zauren Fiqhu wanda ke dauke da labarin tashin Alqiyamah da nauye-nauyenta.

Tsakanin busa ta farko da ta biyu tsawon shekaru arba'in ne. Sannan Allah zai sanya sararin samaniya tayi wani irin ruwa mai kama da maniyyin mazaje, wanda daga gareshi ne za'a sake gina halittar jikkunan halittu. Zasu rika tsirowa daga Qasa kamar yadda shuka ke tsirowa.

Dama tun lokacin da jikkunan mutane suka narke suka zama Qasa, akwai wani Qashi wanda ba ya narkewa. Wato Qashin gadon baya (Vitabrae) to daga gareshi ne sauran Qasusuwa zasu tsira, sai kuma halittar jiki ta ginu, sai kuma jiran lokacin da Qasar zata tsage ta fidda nauye-nauyen dake cikinta.. Allahu Akbar!!

Bayan dukkan jikkuna sun gama ginuwa acikin Qaburburansu, Allah Madaukakin Sarki zai sake raya manyan Mala'ikunsa Jibreelu, Mika'eelu, Israfeelu da Malakul Mauti (alaihimus salam).

Zai umurci Mala'ikan nan ma'abocin Qaho (Israfeel) cewa ya sake yin busa acikin Qahon. Nan take sai dukkan rayuka su koma jikkunan ma'abotansu.. Sai kuma fitowa daga Qabari..

Dama Ubangiji (SUBHANAHU) ya fa'da acikin Alqur'ani cewa "DA HALITTARKU DA TASHINKU BASU ZAMANTO BA, FACHE KAMAR RAI GUDA.." (Wato yawanku ba zaisa Allah ya gagara tashinku ba, babu abinda keda wuya gareshi. Idan yazo kasheku ko rayaku, kalmarsa "KUN FAYAKUNU" ce).

Ibnu Katheer yace "Qarshen wanda zai mutu (daga cikin halittu) shine Mala'ikan mutuwa. Sai rayayyen sarkin da shine na farko kuma na Qarshe, Shi kadai zai wanzu.

Daga nan ne Ubangiji Mabuwayi zai yi tambayar da babu mai amsawa. Zai ce "MULKI AWANNAN RANAR NA WANENE?".

Zai yi wannan tambayar har sau uku amma babu mai amsawa, sai Shi zai bama kansa amsa yace "(MULKIN) GA ALLAH NE MAKADAICI MAI RINJAYE". Ma'anarsa wato "NINE MAKADAICI TUN FARKO, KUMA NA RIGA NA RINJAYI DUKKAN KOMAI, KUMA NA HUKUNTA QAREWA AKAN DUKKAN KOMAI".

Daga nan sai Allah ya raya bawansa Mala'ika Israfeelu, Sannan ya umurceshi cewa ya busa wannan Qaho. Wato busa ta uku kenan wacce idan yayita sai dukkan jikkunan nan su fito daga Qaburburansu.

Awannan ranar babu wani girma ko mulki ko sarauta ko karfi na duniya wanda zai amfanar da ma'abocinsa.. Koda ceto ba zai yiwu ba sai bayan Allah yayi izini kuma ya yarda.. ALLAHU AKBAR!!

An gabatar da wannan karatu a Zauren Fiqhu Whatsapp ranar 27/07/2018  14/11/1439.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI