YA ALLAH ABIN DOGARO ABIN NEMA


Ya Allah lallai duk wanda ya samu girma dominka ba zai Qaskanta ba. Domin kai ne AL-AZEEZU Mabuwayin da ba ya Qaskanta, kuma babi mai iya rinjayarsa.

Ya Allah duk wanda ya shiryu da kai ba zai 'bata ba. Domin kai ne ALHADIY, Mai shiryar da bayinsa ta yadda yaso.

Ya Allah lallai duk wanda ya yalwatu da kai, ba zai samu Qaranta ba. Domin kai ne ALWASI'U. Mai yalwar da babu Qarewa.

Ya Allah lallai duk wanda ya Qarfafa dakai ba zai raunana ba. Domin Kai ne ALQWIYYU Mai Qarfin da ba ya rauni ba ya gajiyawa.

Ya Allah lallai duk wanda ya Wadatu da Kai ba zai bukatu ga waninka ba. Domin kai ne ALGANIYYU.  Mawadacin da ba ya talauta. Kuma taskarsa ba ta Qarewa.

Duk wanda ya Dogara da kai ba zai ta'be ba. Duk wanda ya zamanto Kai ne Mafakarsa to ba zai tozarta ba. Kuma duk wanda yayi riko da kai to lallai hakika ya shiryu zuwa ga Tafarki Madaidaici.

Ya Allah don Qarfin ikonka ka isar mana akan duk wanda ya zaluncemu. Ka kiyayemu daga kaidin Makiya da Mahassada.

Don buwayar Qarfinka kar kasa Makiyanmu su ga bayanmu. Ka kiyayemu daga dariyar Makiya.

Ya Allah don Qarfin Wadatuwarka daga dukkan halittunka, Ka tsaya mana ka isar mana, Kar ka jinginar damu bisa kanmu.

Ya Allah don wadatuwar Shiriyarka, Ka shiryi yaranmu Qanana da iyalanmu tare damu baki daya.

Ka kiyayemu daga fizgar Shaitanun Mutane da Aljanu, Ka Qarfafemu da Kulawarka ta Musamman akan dukkan lamuranmu.

Kayi salati gwargwadon adadin bugun numfashin dukkan halittunka, da adadin motsinsu da shirunsu, bisa Annabinka Zababbenka Shugabanmu Muhammadu tare da iyalan gidansa masu alfarma da Sahabbansa masu albarka. Ka dawwamar da Salatin Gwargwadon dawwamar Mulkinka.

Albarkacin wannan salatin ka yaye damuwar dukkan daliban  Zauren Fiqhu da duk wanda ya karanta rubutun nan, da kuma dukkan Musulmai baki daya.

Ka gafarta ma Mahaifanmu da Malumanmu da 'Yan uwanmu rayayyu da matattunsu. Ka sanya samun Yardarka ya zama babban burinmu ako yaushe. Kuma ka sanya mana Ikhlasi acikin dukkan ayyukanmu.

DAGA ZAUREN FIQHU (14 JULY 2016) 09-10-1437).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI