KWARJININ MANZON ALLAH (SAWW)

Annabi (saww) shine mafi kyawu mafi kwarjini acikin dukkan bayin Allah. Wannan kwarjinin nasa shine ya lullube kyawun. Shi yasa Mutane basu fitinu da kyawunsa kamar yadda ya faru ga Annabi Yusuf (as) ba.

Manyan Sahabbansa irin su Sayyiduna Abubakar da Umar (ra) basu iya bayanin siffofinsa sosai saboda kwarjininsa ya hana su Qare masa kallo.

Idan Suna zaune agabansa, dukkaninsu sukan sunkuyar da kansu Qasa ne. Basu iya cira kai su kalleshi, basu yin surutu ko hayaniya atsakaninsu. Hasali ma basu iya yin magana har sai in bukatar hakan ta taso.

Sayyiduna 'Amru bn Al-Aas (ra) yace "Idan muka zauna agaban Manzon Allah (saww) mukan shiga cikin wasu irin yanayi guda biyu masu girma :

- Yanayi na farko shine muna son mu 'daga kai mu kalleshi saboda tsananin Soyayyarmu gareshi da kuma farin cikin kasancewa tare dashi.

- Yanayi na biyu kuma, Kwarjininsa yakan lullubemu har sai munji ba zamu iya yin koda motsi agabansa ba.  (saww). Hakika na zauna agabansa sau da yawa. Amma wallahi ba zan iya siffanta muku Shi ba (saww).

Wata Sahabiyarsa mai suna Qeelah bintu Makhramah (ra) tace : "Na taho wajen Manzon Allah (saww) alhali yana zaune. Yayin da na kalleshi (saww) ya sunkuyar da kansa atsakanin Sahabbansa, Sai Jikina ya fara rawa, (Kwarjininsa ya kamani).

Sai Wadanda ke tare dashi suka ce masa "Ya Rasulallahi waccen Matar fa jikinta rawa yakeyi". Sai Annabi (saww) yayi mun magana ba tare da ya kalleni ba, duk da cewa ina kusa dashi.

Yace "KI NUTSU YA KE BAIWAR ALLAH". Yayin da ya fadi haka sai naji tsoron da nakeji azuciyata ya tafi..

Ibnu Sa'adin ya kawo wannan Qissar acikin Tabaqatul Kubra.

Ya Allah ka azurtamu da ganin hasken fuskar nan tasa mai kwarjini. Ya Allah ka Qara mana Sonsa da biyayyarsa da ganin Girmansa (saww).

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (19-04-2016)

ZA'A IYA SAMUNMU AKAN SHAFIN FACEBOOK :  Zauren Fiqhu Facebook

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI