MU SAN ANNABINMU (26)
Salati da amincin Allah su tabbata bisa Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan mabiyansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako. Acikin wannan darasin na Zauren Fiqhu zamu dora daga inda muka tsaya acikin tarihin Manzon Rahama (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). YAQIN HAMRA'UL ASAD : Washegarin dawowa daga yaqin uhudu sai Manzon Allah (saww) yayi tunanin watakil mushrikan Quraishawa su sake kawo hari garin madeenah don haka yayi nufin fita domin sake tararsu a sake wani sabon gumurzu don a nuna musu cewa har yanzu fa musulunci yana nan da Qarfinsa. Ashe kuwa shi Abu Sufyan shugaban dakarun Quraishawa ya daura niyyar dawowa din don Qara kawowa hari akan Musulmai, akan hanyarsa sai ya hadu da wani mutum mai suna Ma'abadu 'dan Ubayyu Alkhuza'iy. Sai Abu Sufyan din ya tambayeshi "Meye labarin abinda ke bayanka?". Sai yace masa "Ya kai Abu Sufyan, yi sauri ka guje daga garesu domin hakika sun tanadi makama