MU SAN ANNABINMU (03)

Da sunan Allah Makadaici, Salati da aminci su tabbata bisa Fiyayyen Halittu tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da dukkan bayin Allah Salihai.

SHAYARWARSA (SAWW)  :

Farkon wacce ta shayar dashi aduniya ita ce mahaifiyarsa Nana Aminatu 'yar Wahb, daga nan sai wata baiwar baffansa Abu Lahab wacce ake kira Thuwaibatul Aslamiyyah (rta) ta shayar dashi itama. Kuma dama Abu Lahab din ya 'yantar da ita tun bayan haihuwar Manzon Allah (saww) alokacin da tazo yin albishiri gareshi cewa Matar 'dan uwansa ta haifi 'da namiji.

Sai kuma Haleematus Sa'adiyyah itama ta shayar dashi. Kuma ta dalilin wannan shayarwar ta samu daukaka da fifiko da yalwar arziki. Gidanta ya cika da albarka da arziki da ni'ima saboda albarkacin kasancewar Annabi (saww) tare da ita.

Kuma yana daga cikin girmamawar da Allah yayi masa, dukkan matayen da suka shayar dashi sun karbi addininsa (saww). Koda yake akwai riwayar da tazo da akasin haka, amma riwayar musuluntar tasu tafi Qarfi kuma gareta ne Malamai suka fi karkata.

Salatin Allah da amincinsa Madawwami su Qara tabbata bisa Annabin Rahma tare da iyalan gidansa da Sahabbansa masu albarka.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (28/10/2018 19/02/1440).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI