HANYOYIN KANKARAR ZUNUBAI (1)

TUBA DAGA DUKKAN ZUNUBAI

Daliban Zauren Fiqhu da sauran jama'ar musulmai, Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Wannan sabon jerin karatu ne wanda yake kunshe da wasu hanyoyin samun kankarar zunubai da lada mai yawa. Zai  rika zuwa muku tare da ayoyi da hadisai ingantattu. In shaAllah.

Hanya ta farko wacce zaka bi amatsayinka na bawan Allah domin neman kusanci da mahaliccinka ita ce hanyar tuba daga duk wani zunubi da kasan kana aikatawa, Qananan zunubai da manyansu in dai ka tuba domin Allah, to zai karbi tubanka cikin karamcinsa kuma ya gafarta maka laifukanka.

Ya fa'da acikin littafinsa mai girma yace : "KU TUBA ZUWA GA ALLAH BAKI DAYANKU YA KU MUMINAI, TSAMMANIN TABBAS ZAKU RABAUTA".

Suratun Nur ayah ta 31.

Kuma kada girman zunubanka ko kallon yawan laifukanka, ko laifukanki ya hanaka, ko ya hanaki tuba. Hakika babu abinda yake gagarar Ubangiji. Kada ku manta fa Allah yayi kira garemu ta hanyar Annabinsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace :

"KACE : YA KU BAYINA WADANDA SUKAYI BARNA BISA KAWUNANSU, KADA KU DEBE TSAMMANI DAGA SAMUN RAHAMAR ALLAH. HAKIKA ALLAH YANA GAFARTA ZUNUBAI BAKI DAYA, HAKIKA SHI SHINE MAI GAFARA MAI JIN QAI".

Koda shirka kakeyi, in dai wa'azi yazo maka, kaji tsoron Allah ka dena ka tuba kafin mutuwarka to Allah zai gafarta maka. Ayar nan ta cikin suratun Nisa'i tana nufin wadanda suka mutu suna shirka basu tuba ba, to sune wadanda Allah ba zai gafarta musu ba. amma wand ya tuba kafin mutuwarsa zai samu gafarar Allah. (aduba manyan  litattafan tafsiri).

Manzon Allah (saww) yace Allah yace "Ya kai Dan Adam! Mutukar kai kana kirana kuma kana kwadayin rahamata zan gafarta maka abinda ke gareka (na laifi) kuma ban damu ba. Ya kai Dan Adam! Koda yawan zunubanka sun ta'bo sararin samaniya kuma ka nemi gafarata zan gafarta maka.

Ya kai 'Dan Adam, da ache kai zaka zo min da cikin doron Qasa na zunubai, sannan ka ha'du dani alhali baka ha'da kowa dani wajen bauta, wallahi da sai nazo maka da cikinta na gafara".

(Tirmidhiy ne ya riwaitoshi).

Hakanan Ibnu Maajah ma ya ruwaito Manzon Allah (saww) yana cewa "MAI TUBA DAGA ZUNUBI KAMAR DAI WANDA BASHI DA ZUNUBI NE".

Kuma yace "DA ACHE ZAKUYI TA AIKATA LAIFI HAR LAIFUKANKU SU TA'BO SARARIN SAMANIYA, SANNAN KUKA TUBA, DA SAI (ALLAH) YA KARBI TUBANKU".

Tuba tana da sharuda guda uku ko hudu kamar haka :

1. Yin nadama akan abubuwan da ka aikata a baya.

2. Daukar niyyar cewa har abada ba zaka sake komawa cikin zunubin ba.

3. Nisantar aikin sa'bon, da kuma duk wasu hanyoyi ko abokan da zasu iya komar dakai cikin zunubin.

4. Idan laifin ya shafi hakkin wani ko wasu, to wajibi ne ka nemi yayewarsu, ko kuma ka mayar musu da hakkokinsu.

Allah yasa mu dace da samun rahamarsa don albarkar Alqur'ani.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (08/04/2019 03/08/1440).

Ku tura zuwa ga sauran groups da contact dinku ba tare da chanza komai ba. Domin neman shawarwari ko tambayoyi ku tuntubi zauren Fiqhu ta email zaurenfiqhu@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI