MU SAN ANNABINMU (24)


Da Sunan Allah Mai Girma, salati da amincinsa su tabbata bisa bawansa mafi girma, Annabinmu Muhammadu tare da Iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa masu girma.

YAKOKIN ANNABI (SAWW) :

Yakokin da Manzon Allah (saww) yayi azamaninsa, ba wai yana yinsu ne domin daukar fansa ko son zubar da jini ba. A'a yakokin nasa sun kasance ne domin mayar da kaidin abokan gaba da ladabtarwa ga duk wani mai ta'addanci, da kuma kira zuwa ga addinin Allah.

Annabi (saww) yayi yakoki da dama kafin badar da kuma bayanta, domin amintar da garin Madeenah da kuma bayar da kariya gareta daga hare-haren kafirai.

Akwai yakokin da ya samu halarta, sun kai kamar guda ashirun da bakwai ko da takwas. Akwai kuma wasu da dama wadanda bai je ba amma ya tura da rundunoni karkashin jagorancin amintattu daga cikin Sahabbansa.

YAQIN BADAR :

Manzon Allah (saww) ya samu labarin gabatowar wani ayarin fatauci na Quraishawa mai kunshe da rakuma dubu dauke da kayan fatauci, Kuma Abu Sufyan ne yake jagorantar tafiyar.

Sai Manzon Allah (saww) ya umurci Sahabbansa cewa "KU FITA ZUWA GARESU WATAKIL ALLAH YA KARBA MUKU ITA".

Shi kuwa Abu Sufyan (shugaban ayarin Quraishawa) yayun da labari ya iso gareshi cewa Manzon Allah (saww) ya fito da jama'arsa domin tarar ayarinsu, sai ya aika ya sanar wa mutanen makkah (Quraishawa) cewa su fito domin kare dukiyoyin dake cikin ayarinsu. Sannan kuma ya dauki hayar wani mutum wanda yabi dashi ta wata hanyar wacce ba'a santa sosai ba, har dai ya tseratar da ayarin nasu.

Su kuwa abangaren Quraishawa, yayin da labari ya iskesu sai suka kira taron gaggawa atsakaninsu. Suka yanke shawarar cewa lallai dole su fita su yaqi Manzon Allah (saww) domin kare ayarinsu. Don haka sai manyan garin suka fito kwansu da kwarkwatarsu, kowa da shirin yaqi.

Abu Sufyan ya basu shawarar cewa su koma gida tunda an tseratar da ayarin nasu. Amma Abu Jahal (L.A) ya kafe kuma yayi rantse da gumakansa cewa sai yaje filin badar ya zauna tsawon kwanaki uku yasha giya, ya saurari kida da wakoki, yadda har sai labarin ya watsu atsakanin  sauran Qabilun larabawa domin suji tsoro da kwarjinin Quraishawa.

Shi kuwa Manzon Allah (saww)  ya fito tare da Sahabbansa guda dari uku da goma sha uku (313) ko kuma 315 a qata riwayar. Tare da takubba goma sha shida, dawakai uku, da rakuma saba'in.

Su kuwa abangaren Mushrikan Quraishawa, aun fito tare da mutum dari tara da hamsin (950)  kowanne da cikakken shirin yaqi da kayan yaqi, tare dasu kuma akwai rakuma dari bakwai (700) da dawakai dari (100).

Yayin da dakarun biyu suka hadu da juna, an fara gwabza yaqin ne ta hanyar salon fito-na-fito (wato Mubarazah). Mutum uku daga bangaren kafirai suka fara fitowa suka bukaci wasu su fito daga bangaren Muminai. Bayan Muminan sun samu nasarar kashesu sai yaqi ya rinchabe.

Allah Madaukakin Sarki ya turo da rundunonin Mala'iku domin taimakon Annabinsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) kuma nasara ta tabbata ga muminai.

Daga bangaren Muminai mutum goma sha hudu ne sukayi shahada. A bangaren kafirai kuma an kashe mutum saba'in daga cikin manyansu, kuma an kama wasu saba'in din amatsayin fursunonin yaqi. Kuma daga cikin wadanda aka kashe din har da babban makiyin Allahn nan wato Abu Jahal 'dan Hisham.

Muhimmancin Yaqin badar bashi da iyaka acikin tarihin musulunci. Domin dashi ne musulunci ya fara nuna Qarfinsa, kuma daga kansa ne tutar musulunci ta kafu.

Anan zamu tsaya sai a karatu na gaba kuma zamu dora in shaAllah. Salati da amincin Allah au tabbata bisa Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa da matayensa da dukkan Sahabbansa baki daya.

An gabatar da karatun ne a Zauren Fiqhu Whatsapp ranar 11/04/2019 06/08/1440.

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI