MU SAN ANNABINMU (11)

Da sunan Allah Mamallakin komai da kowa, Salatinsa da amincinsa su tabbata ga Mabudin alkhairansa, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa baki daya.

SABUNTA GININ KA'ABAH
*************************
Yayin da shekarun Manzon Allah (saww) suka cika talatin da biyar aduniya, anyi wani ruwa mai yawa acikin garin Makkah wanda ta sanadiyyar ambaliyarsa ya kwararo ya cika dakin Allah mai alfarma (KA'ABAH) har sai da bangwayenta suka tsattsage.

Saboda tsoron rushewarta sai Quraishawa suka yanke shawara atsakaninsu cewa zasu rushe ginin sannan su sake mayar dashi kamar yadda yake.

Tare da bayar da gudunmuwa daga mafi tsarkin dukiyarsu, sunyi nasarar mayar da ginin. To amma yayin da aka zo wajen mayar da Baqin dutsen nan (Hajarul Aswad) wanda ke maqale ajikin dakin Ka'abah, sai suka samu sa'bani atsakaninsu akan shin wanene zai dauki dutsen ya sanyashi awajensa, saboda alfahari da girman dake cikin wannan.

Daga karshe sai suka yanke shawarar cewa duk mutumin da ya fara shigowa cikin farfajiyar Masallacin, shine zai yanke hukunci atsakaninsu. Ana cikin haka sai suka hangi Annabi (saww) ya shigo. Sai murna ta 'barke atsakaninsu suna cewa "Ga mai gaskiya da amana nan ya shigo! Ga mai gaskiya da amana nan ya shigo!!".

Da zuwansa sai ya sanya aka shimfida wani mayafi a Qasa sannan ya dora dutsen bisa mayafin, kuma ya umurci mutum guda daga kowacce Qabila yazo ya rike gefen mayafin. Suka dauka suka taho har sai da suka zo jikin dakin, sannan Annabi (saww) ya sanya hannayensa masu daraja ya dauki dutsen ya sanyashi a mazauninsa na asali. Allahu Akbar!!!.

Dawwamammun Salatai da amincin Allah su tabbata bisa Annabi Muhammadu da iyalan gidansa da matayensa da Sahabbansa da mabiyansa da mataimakansa da dukkan masu shauqi cikin begensa da tunaninsa, gwargwadon gudanuwar ruwa da iska, dare da rana.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (11/03/1440 19/11/2018).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI