MU SAN ANNABINMU (23)

Da sunan Allah Makadaici abun bauta. Salati da amincinsa su tabbata ga babban bawansa, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa da dukkan Sahabbansa.

SHIRYA ZAMAN MADEENAH :

Kamar yadda na fa'da muku acikin darasi na 22,  ainahin sunan garin Yathriba amma bayan isowar Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) sai sunanta ya koma "Madeenatur Rasool" (Birnin Manzon Allah) ko kuma Al Madeenatul Munawwarah (Birni abin haskakawa) wato ta haskaku da hasken Manzon Allah (saww) kenan.

To bayan isowarsa sai dukkan lamuran garin suka koma hannunsa. Shine Sarki, shine Alkali, shine kwamandan yaqi, dama kuma shine jagoran addini ga dukkan masu rabo. Kuma ya fara gudanar da muhimman ayyuka guda uku kamar haka :

1. Ginin Masallacinsa.
2. Ha'da 'yan uwantaka atsakanin Sahabbansa na Madeenah (Al ansar) da kuma wadanda suka yiwo hijirah zuwa garesu (Al Muhajirun).
3. Qulla alkawuran zaman lafiya tsakanin al'ummarsa da kuma Yahudawan dake zaune acikin garin Madeenah da kewayenta.

MASALLACI : Ya ginashi ne domin ya zama muhallin gudanar da ibadah, da kuma isar da sakon manzanci, kuma ya kasance cibiyar haduwar muminai domin tattauna muhimman lamuran addini da zamantakewarsu.

'YAN UWANTAKA : Ya sanya ma kowanne mutumin Madeenah 'dan uwa daga mutanen Makkah wanda shi mutumin madeena din zai taimakeshi da abinci da wajen zama da kuma dukiyar da zai fara juyawa kafin ya saba da zaman garin.

ALKAWURA : Ya kulla alkawarin zaman lafiya da kyakkyawar makobtaka tsakaninsa da Qabilun Yahudawan nan guda uku dake Madeenah wato Banu Qainuqa'a, Banu Quraizah, da Banun Nadheer.

To wadannan abubuwan guda uku sune manyan ginshikan ginin daular musulunci wacce daga wannan garin na Madeenah kafin shekaru hamsin sai da ta mamaye dukkan yankunan larabawa har ta tsallaka sauran Qasashe da dauloli har ta kawar da daular farisa wacce tafi shekaru dubu tana mulki aduniya.

JUYA ALQIBLAH :

Tun kafin hijirah Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya kasance yana kallon baitul maqdis ne (wato Masallacin Kudus) yaci gaba kuma da kallonta amatsayin Alqiblar ibadah bayan hijirarsa har tsawon watanni goma sha shida amma ko yaushe yana kallon sararin samaniya tare da fatan Allah ya juyar masa da mafuskantar ibadarsa zuwa ga dakin Allah mai alfarma na Makkah (wato Ka'abah).

Allah kuwa ya amshi rokonsa yayi masa umurni cewa ya juya zuwa ga dakin Allah mai alfarma dake Makkah. Wannan ya faru ne aranar sha biyar ga watan sha'aban acikin shekara ta biyu bayan hijirah.

Allah yace masa : "HAKIKA MUN GA JUYAR FUSKARKA ZUWA GA SARARIN SAMA, YANZU ZAMU JUYAR DAKAI ZUWA GA ALKIBLAR DA ZAKA YARDA DA ITA" (WATO WACCE RANKA YAFI SO).

Sallar farko wacce Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yayi bayan saukar wannan wahayin ita ce sallar la'asar. Kuma masallacin Banu Haritha sun kasance suna cikin sallah sunyi raka'a biyu kenan sai aka sanar dasu maganar juyawar Alqiblah sannan suka juya. Kuma wannan masallacin nasu ayanzu shi ake kira Masjidu Qiblataini (Masallaci mai Alqibla biyu).

Anan zamu tsaya sai acikin darasi na gaba in shaAllahu zamu shiga tarihin Yakokin Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

An gabatar da karatun ne a Zauren Fiqhu Whatsapp ranar talata 02/04/2019 26/07/1440

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI