MU SAN ANNABINMU (04)

Godiya ta tabbata ga Allah Mamallakin zukata da hankula, wanda ya zabi zukatan wasu daga cikin bayinsa kuma ya karkatar da zukatansu zuwa ga shagaltuwa da kokarin sani da koyi da neman cikar soyayyar Manzonsa wanda ya aiko zuwa ga dukkan halittu (saww).

Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da bai ta'ba magana bisa son rai ba, fache bisa wahayi daga Ubangijinsa.

TSAGAWAR KIRJINSA :

Kamar yadda muka ta'ba bayani acikin wani darasinmu na Zauren Fiqhu Whatsapp, an tsaga Kirjin Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ne har sau hudu alokuta daban daban. Kuma ga takaitaccen bayanin yadda kowanne ya faru :

NA FARKO : Lokacin da ya cika shekaru hudu aduniya, sai Ubangijinsa (SWT) ya turo masa Mala'iku guda biyu wato Jibreelu da Meeka'ilu (amincin Allah ya tabbata garesu). Suka zo suka tarar dashi alokacin yana kiwon tumakin Halimatus Sa'adiyyah tare da sauran yaranta. Mala'ikun nan suka kwantar dashi suka tsaga qirjinsa suka fito da zuciyarsa madaukakiya, suka tsagata suka fitar da wani abu, sannan suka wanketa da wani ruwa mai sanyi, suka cikata da ilimi da hikima, sannan suka mayar da ita yadda take.

Kuma yayin fitarwan sai Mala'ika Jibreelu yace "Wannan shine rabon shaidan daga gareka". (Kamar yadda Bukhariy da Muslim suka ruwaito).

TA BIYU : Ta faru ne dab da lokacin cikarsa shekarun balaga.

TA UKU : Ta faru ne dab da lokacin da za'a fara yi masa wahayi.

TA HUDU : Ta faru ne acikin daren da akayi Isra'i da Mi'iraji dashi zuwa ga halarar Ubangijinsa (Subhanahu wa Ta'ala).

Ya Allah kayi salati da aminci bisa Ma'abocin wankakkiyar zuciya da fararen gabbai, Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa da Salihan bayinka baki daya. Ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP 1 07064213990 (30/10/2018  21/02/1440).

Comments

Popular posts from this blog

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYIN MAZA DA NA MATA

MAGANIN KAIKAYIN GABA

ADDU'AR NEMAN KARIYA DAGA SHARRIN MAHASSADA DA AZZALUMAI